Mun lalata kwayar Tramadol ta Naira tiriliyan 2 – NAFDAC
Hukumar ta ce ta sami nasarar ne a cikin shekara hudu.
Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta ce ta lalata kwayar maganin Tramadol da darajarta ta kai zunzurutun kudi har Naira tiriliyan biyu a cikin shekara hudu.
Shugabar Hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bayyana hakan a Abuja ranar Laraba, lokacin da take jawabi ga manema labarai kan bikin cikarta shekara hudu tana jagorancin hukumar.
- Rasha za ta taimaki Najeriya ta yaki ta’addanci
- Masu garkuwa da mutane sun bukaci Sigari da Tabar Wiwi a matsayin fansa
A cewarta, hukumar ta kuma samu nasarar lalata jabun magunguna da darajarsu ta kai Naira biliyan takwas a tsawon lokacin.
Ta ce, “Domin ci gaba da tabbatar da lafiyar al’umma, hukumarmu ta lalata jabu, gurbatattu, haramtattu da kuma kayayyaki marsa sa kyau na sama da Naira 8,000,260,000, a sassa daban-daban a fadin kasar nan.
“Muna kuma ci gaba aikin rage cunkoso a dakunan ajiyarmu da ke Apapa a Jihar Legas, wadanda suka cika tun shekarar 2013.”
Ta kuma ce akwai kalla shari’u kimanin 20 da hukumar take fafatawa da masu ta’ammali da jabun magunguna, kuma akasarinsu an yanke musu hukuncin dauri, wasu kuma na biyan tara.
Farfesa Adeyeye ta kuma ce NAFDAC ta haramta wa wasu kamfanonin kasar Indiya guda biyu kawo magungunansu Najeriya da ma kamfanin da yake yi musu dillanci a nan.