Mun makara
Wani barawo ne ya shiga wani gida sata, yana zuwa kai tsaye sai ya wuce daki sai ya tarar da maigidan ya mutu gawarsa tana kan gado. Yana kokarin ya fito ya gudu sai ya ji mutane suna kokarin shigowa dakin domin daukar gawar zuwa makabarta. Nan take sai ya dauki wata sanda ya labe […]
Wani barawo ne ya shiga wani gida sata, yana zuwa kai tsaye sai ya wuce daki sai ya tarar da maigidan ya mutu gawarsa tana kan gado. Yana kokarin ya fito ya gudu sai ya ji mutane suna kokarin shigowa dakin domin daukar gawar zuwa makabarta. Nan take sai ya dauki wata sanda ya labe a dakin. Da mutanen nan suka zo sai liman ya fara shiga, barawon da ke labe ya kwantara masa sandar. Liman ya fito da gudu, mutane suka tambaye shi abin da ya faru? Sai ya ce masu: “Ai mun makara, domin an fara masa hisabi.”