Mun mayar da yara miliyan 1.5 makaranta a Borno – Zulum
Gwamnan ya ce adadin yaran na wakiltar kashi 70 na yara miliyan 2.2 da aka gano ba sa zuwa makaranta a jihar.
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce gwamnatinsa ta mayar da yara sama da miliyan 1.5 makarantu a jihar.
Ya ce adadin yara da aka mayar makarantu na wakiltar kashi 70 na yara miliyan 2.2 da aka gano ba sa zuwa makaranta a jihar.
- Mutum 6 sun mutu a wani sabon hatsarin mota a Jigawa
- Boko Haram sun fille kan masunta 14 a kan iyakar Najeriya
Gwamnan, ya bayyana hakan ne ranar Talata, lokacin da ya ƙaddamar da makarantar Sakandaren Gwamnati ta Mairi, wanda Daraktan Bankin Duniya, Dokta Ndiame Diop, ya halarta.
Ya ƙara da cewa, cikin shekaru biyar da suka gabata, gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen saka yara makaranta, inda ya bayyana cewa saura yara 700,000 za a mayar da su makaranta nan ba da jimawa ba.
“Mun gina makarantu 104, mun gyara ajujuwa 2,931, sannan mun raba kayan karatu kyauta, wanda ya haɗa da littafan rubutu miliyan 20, littattafan karatu miliyan biyu, kayan makaranta miliyan 15, jakunkunan makaranta 700,000, da kuma wasu miliyoyin kayayyaki,” in ji Gwamnan.
Ya kuma bayyana cewa shirin ciyar da ɗalibai zai shafi yara 50,000, yayin da gwamnati ta raba kekuna 10,000 ga ɗalibai a yankunan karkara don rage musu wahalar zuwa makaranta.
Dangane da matasan da suka wuce shekarun makaranta, gwamnan ya ce gwamnati ta mayar da hankali kan ilimin fasaha da sana’o’i (TVET).
“Mun kafa Cibiyoyin Sana’o’i guda biyar, Makarantun Sana’o’i na Mata da ’Yan Mata guda biyu, sannan mun gyara wasu cibiyoyin koyar da sana’o’i guda tara.
“Manufarmu ita ce horar da matasa 5,000 a duk shekara, don su samu abin dogaro da kansu da rage rashin aikin yi,” in ji shi.
A nasa ɓangaren, Daraktan Bankin Duniya, Dokta Ndiame Diop, ya yaba da ƙoƙarin Jihar Borno wajen farfaɗo da ilimi duk da matsalar tsaro.
Ya ce bankin ya taimaka wajen gina makarantun sakandare 41 da gyara wasu makarantu 392 a jihar.
“Wannan makaranta wata shaida ce ta jajircewar gwamnatin Borno wajen sake bunƙasa fannin ilimi duk da ƙalubalen da ta ke fuskanta.
“Muna alfahari da wannan ƙoƙari kuma za mu ci gaba da tallafa wa gwamnati,” in ji Dokta Diop.