Mun noma shinkafar da za ta iya ciyar da Najeriya – RIFAN

Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN), reshen Jihar Kaduna, Alhaji Muhammad Numbu ya ce Jihar Kaduna ta noma shinkafar da za ta iya ciyar da fadin jihar da kuma kasa baki daya. Shugaban, ya yi kira ga manoman shinkafa su kara tashi tsaye wajen inganta harkar noma tare da biyan rancen da gwamnati ta […]

Mun noma shinkafar da za ta iya ciyar da Najeriya – RIFAN

Tambarin RIFAN

Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN), reshen Jihar Kaduna, Alhaji Muhammad Numbu ya ce Jihar Kaduna ta noma shinkafar da za ta iya ciyar da fadin jihar da kuma kasa baki daya.

Shugaban, ya yi kira ga manoman shinkafa su kara tashi tsaye wajen inganta harkar noma tare da biyan rancen da gwamnati ta ba su don bunkasa noman shinkafa, a matakin da ta dauka don karfafa gwiwar manoman.

Shugaban ya yi wannan kira ne yayin da yake ganawa da manema labarai a garin Kafanchan, inda ya ce manoman shinkafa dubu 57 da 386 suka amfana da rancen a fadin Jihar Kaduna.

Ya ce sirrin nasarar noman shinkafar shi ne yadda suka yi amfani da ingantaccen iri da kuma maganin kwari da suka raba wa manoma rance, abin da ya ce ya sa noman ya yi matukar kyau a jihar.

“Duk wanda ya biya rancen da aka ba shi za mu kara masa fiye da abin da aka ba shi da farko. Idan mutum ya karbi rancen da ya noma hekta daya ne za mu ba shi wanda zai noma na hekta biyu nan gaba, amma idan ya dawo da shi,” inji shi.

Ya ce bayan cin nasarar rancen farko sun sake karbar na biyu wanda suke fatar samun abinb da suke so, don haka ya kara nanata kira musamman ga manoman shinkafa daga Kudancin Kaduna su yi kokari su biya bashin da ake bin su don fitar da shi kunya tunda shi ma daga yankin ya fito.

Yayin da ya waiwaya kan matasa, ya gargade su da su rabu da bangar siyasa ko jiran ayyuka masu maiko, maimakon haka, su shigo cikin wadanda za su amfana da bashin noman shinkafa don kama harkar noma ce za ta fisshe su saboda irin alherin da ke cikinta.

“A yanzu ana shirye-shiryen wani sabon rancen ne tare da hadin kan Babban Bankin Najeriya (CBN) da Bankin Manoma (BOA) da bankin Unity Bank wanda hatta sababbin manoma na maraba da su domin cin gajiyar rancen da manufarsa ita ce bunkasa noman shinkafar da kasa za ta rika dogara da ita da kuma fitar da ita zuwa kasashen waje, kuma hakan na bukatar karin manoman shinkafa a Najeriya baki daya,” inji shi.

A karshe ya yaba wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Kaduna Malam El-Rufa’i da Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa Alhaji Aminu Goronyo bisa namijin kokarin da suke nunawa tare da bayar da goyon baya don bunkasa noman shinkafa don cimma burin Najeriya a harkar noma a duniya.