Mun rasa dukiya ta sama da Naira biliyan 26 a rikicin Jos – Shehu Musalla
Shugaban kungiyar Jasawa ta kasa Alhaji Shehu Ibrahim Musalla ya ce sun yi asarar daruruwan mutane da dukiya ta sama da Naira biliyan 26 a rikicin da aka yi a garin Jos a ranar 28 ga Nuwamban shekarar 2008, lokacin zaben kananan hukumomin jihar. Alhaji Shehu Musalla ya bayyana haka ne a lokacin da yake […]

Shugaban kungiyar Jasawa ta kasa Alhaji Shehu Ibrahim Musalla ya ce sun yi asarar daruruwan mutane da dukiya ta sama da Naira biliyan 26 a rikicin da aka yi a garin Jos a ranar 28 ga Nuwamban shekarar 2008, lokacin zaben kananan hukumomin jihar.
Alhaji Shehu Musalla ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wurin addu’o’in tunawa da wadanda suka rasu a rikicin karo na biyar da aka gudanar a Jos.
Ya ce “A tarihin al’ummar Jos ba mu taba samun lokacin da muka fada cikin bala’i kamar wanda muka shiga a lokacin rikicin na ranar 28 ga Nuwamban shekarar 2008. Don haka muka kebe wannan rana a kowace shekara don yin addu’o’i da karatun Alkur’ani da jawabai kan abin da aka yi mana a wannan rana.”
Ya ce bayan rasa daruruwan mutane har yau ana da tsare da mutanensu a gidajen kurkuku wadanda ke tsare ba tare da an kama su da wani laifi ba.
Alhaji Shehu Musalla ya ce tunda wannan abu ya faru har zuwa wannan lokaci, babu wani taimako daga kowane gefe na gwamnati da suka samu. Kuma wadanda suka yi wannan tu’annati babu daya da aka kama har zuwa yanzu.
Ya nuna farin cikin kan zaman lafiyar da aka fara samu a garin Jos. Ya ce, “Wannan zaman lafiya da muka fara samu wani abu ne da muke alfahari da shi. Don haka ina kira ga al’ummar Jos su ci gaba da hakuri da juna, su ci gaba da kokarin ganin an tabbatar da zaman lafiyar da aka samu.”
Taron wanda aka gudanar a karkashin shugabancin Babban Limamin Jos, Sheikh Balarabe Dawud ya sami halartar Turakin Jos Alhaji Garba Abdulkadir da wakilin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar da dimbin Jasawa daga wurare daban-daban na Najeriya.