Mun rasa mahaifiya da ’yan uwanmu cikin kwana 52 — Iyalan Sarkin Zazzau

Iyalan Sarkin Zazzau marigayi Alhaji Shehu Idris sun bayyana jimaminsu kan rasuwar iyalansu uku cikin ɗan gajeren lokaci

Mun rasa mahaifiya da ’yan uwanmu cikin kwana 52 — Iyalan Sarkin Zazzau

Iyalan Sarkin Zazzau, Marigayi Alhaji Shehu Idris, sun bayyana jimaminsu game da rasuwar mahaifiyarsu da ’yan uwansu a cikin kwanaki 52.

Iyalan sun bayyana haka bayan jana’izar ɗan uwansu, Sarkin Dawakin Tsakar Gidan Zazzau, Alhaji Ibrahim Shehu Idris, wanda Allah Ya yi wa rasuwa.

Marigayin ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, a Zariya sakamakon rashin lafiya.

Al’umma da dama ne suka yi dafifin halartar jana’izar marigayin a ranar Litinin a Fadar Sarkin Zazzau.

Marigayin shi ne na huɗu a jerin ’ya’yan marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris.

Sarkin Dawakin Tsakar Gidan Zazzau, ya rasu ne ranar Lahadi ya bar mata biyu da ’ya’ya shida.

An yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 11 na safiyar ranar Litinin, a gidansu da ke Anguwar Rimin Tsiwa a Zariya.

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja

Gwamnan Akwa Ibom ya kori duk Kwamishinoninsa

Rikicin Masarauta: Kotu ta yi watsi da ƙarar Aminu Bayero