Mun sallami cin hanci da rashawa

A wannan makon daya daga cikin masu bayar da gudunmawa ga wannan fili A’isha Usman Liman mai lambar waya 09093467171 ta aiko da mukalarta ce mai take a sama. A sha karatu lafiya: Mun sallame shi, alkadarinsa ya rigaya ya karye, an yi walkiya duhu ya yaye. Mun wurgar da kwallon mangwaro mun huta da […]

Mun sallami cin hanci da rashawa
Mun sallami cin hanci da rashawa

A wannan makon daya daga cikin masu bayar da gudunmawa ga wannan fili A’isha Usman Liman mai lambar waya 09093467171 ta aiko da mukalarta ce mai take a sama. A sha karatu lafiya:

Mun sallame shi, alkadarinsa ya rigaya ya karye, an yi walkiya duhu ya yaye. Mun wurgar da kwallon mangwaro mun huta da kuda, mun saka rigar ’yanci, mun cire rigar kaya, rigar fitina, kuma rigar wulakanci (cin hanci da rashawa).
Kowa dai ya san ma’anar cin hanci da rashawa na nufin zamba cikin aminci ne, domin yarda da aminci da amana ce ke sa ake damka wa wasu kalilan din mutane don su tafiyar da ragamar mulkin mafiya yawan jama’arsu, ganin cewa ba duka za a zame sarki ba, amma maimakon su rike wannan amana da adalci, sai su yi amfani da wannan damar su so kansu fiye da kowa, su rufe ido su yi wadaka da warwaso tare da fantamawa a cikin dukiyar jama’a iya son ransu.
Sanin kowa ne cin hanci da rashawa ba karamin cin kare ba babbaka ya yi a kasarmu Najeriya ba, domin idan muka duba irin barna da nakasun rayuwa da na tattalin arzikin kasa da ya haddasa munin abin sai dai addu’a.
Shin yanzu ashe ya zama laifi ne don an ba ka damar gudanar da al’amuran al’ummarka? Mu dai sai muna ganin kamar ba wani laifi a cikisa illa dama ce ka samu don inganta rayuwar mutanenka. To me ya sa ba ka ganin fifikon da ka samu, kake mantawa da amanar da aka damka maka, ka rasa ganin kaunar da aka nuna maka, ka rumtse ido ka yi sama da fadi da rub-da-ciki a kan dukiyar al’ummarka? Ba komai ke sa haka ba illa tsantsar son kai da ya mamaye zukatan shugabannin al’umma. Shi kuwa son kai ba abin da yake haddasawa illa danniya, ita kuwa danniya ta samo asali ne daga zalunci, shi kuma zalumci rashin adalci yake haddasa shi, shi kuma rashin adalci rashin shugabanci nagari yake haifar da shi a cikin al’umma.
Ashe in kuwa haka ne cin hanci da rashawa an zo iyakarsa, domin Allah cikin ikonSa Ya dubi kwazo da hobbaasarmu na son samar da canji, Ya tabbatar mana da shi cikin sauki, ba za to ba tsammani, Ya wofantar da azzaluman shugabanni, Ya kafa mana adalan shugabannin, wadanda babu rashin adalci a tare da su, kullum fatansu tabbatar da gaskiya  da amana. Cikin haka ne ma suka sa sallamar cin hanci  da rashawa sahun gaba cikin kudirin jadawalin shugabancinsu.
Sai ga shi daga jin an kaddamar da kwamitocin tabbatuwar hakan, wasu ’yan kasa wadanda suke ganin kamar bai kamata a sallami cin hanci da rashawa ba, ko bai kamata a tono tsohuwar badakalar cin hanci da rashawan da aka yi  ba, ko kuma suna gani kamar ya yi wuri a ce an zo ta kan sallamarsa tun yanzu, sai suka kasa zaune suka kasa tsaye don ganin sun hana tabbatuwar hakan.
To, ku sani yanzu kam ta Allah ba taku ba, bakin alkalami ya rigaya ya bushe, sama ta yi wa yaro nisa, mafarauta sun yi sake dan zaki ya girma.
Talakawa mun yi wa kanmu gata, mun zaba wa kanmu shugabanni nagari masu adalci da amana, mun sa rigar ’yanci, mun fara hango hasken rayuwa, mun yi shirin fita duhun danniya da zalunci, don haka ba mai sake kai mu ya baro mu.
Ai idan maye ya manta uwar da ba za ta manta ba. Ba za mu manta bakin talaucin da kuka haddasa mana ba, ba za mu manta fifita kanku da ’ya’yanku da kuka yi a kanmu ba! ’Ya’yanku na karatu mai kyau da inganci namu ’ya’yan na bara da kwasan bola! Abincinku daga kasashen waje, mu kuma taki ma kun kasa wadata mu da shi balle mu ciyar da kanmu! Duk gonakinmu sun koma dajin Allah. Da kun ji cuta ko rashin lafiya sai ku nufi kasashen ketare, mu kuma kun kasa inganta karatun likitocinmu, kun kasa sama wa asibitotanmu magani da kayan aiki. Kun kashe masana’antun da muke samun aikin yi, kun haddasa mana zaman kashe wando, don kawai kuna da bukatar maida matasanmu ’yan bangar siyasarku.
Ga shi nan yin hakan ya haddasa wa matasa mutuwar zuciya da shaye-shayen miyagun kayan maye da sata da fashi da makami, alhalin naku ’ya’yan na Turai suna jin dadinsu ba su da wata damuwa ko daya.
Yanzu ku don Allah wannan bai ishe ku zama abin kunya da da-na-sanin abin da kuka yi ba? Amma shi ne don an ambata muku ku dawo da satar da kuka yi har kuke kame-kame da kamun kafar a kyale ku? To a kyale ku a kan wane dalili, rashin tausayi ko don ku kun fi sauran ’yan kasa?
Magana ta gaskiya ba ku fi kowa ba, hasali ma ba don muguwar hadama da babakerenku da son kanku ba da kowa a kasar nan ya wadata ya azurta.
Don Allah ta yaya ba za mu sallami cin hanci da rashawa ba, wanda a sanadiyarsa  kowane ma’aikacin gwamnati ya manta da ka’idoji da dokokin aikinsa? Abin da ya ga dama shi yake yi, misali a nan ma’aikaci bai san ya yi aikinsa kansa tsaye ba wai sai an ba shi na goro. Ita kuwa lalitar gwamnati ta zama ba rufi, kowa tsawonsa ya kai, sa hannu kawai zai yi ya kamfata iya zalamarsa.
Komai ya tabarbare ya lalace, har rayukan ’yan kasa su ma an salwantar da su wa cin hanci da rashawa, inda ta kai almundahanar da ake yi cikin kudin tsaro ta fi muhimmaci ga jami’an tsaro kan su kiyaye dukiyoyi da rayukan al’ummar kasa.
Fitintinu da rigingimu da zubar da jini da kashe-kashen rayuka da  koma bayan arziki sun addabi kowa a kasarmu a wancan lokacin duk a sanadiyar cin hanci da rashawa.
Kada mu manta fa duk da haka akwai hukumomin da aka kafa na hana cin hanci da rashawar nan, sai dai saboda danniya da bakin zaluncin manyan shugabanninmu, sun hana su katabus, hasali ma sai suka mayar da su karnukan farautarsu, sai wanda gwammanti ba ta yi da shi, za a bincika ko wanda ke kokarin hana ta cin hanci, a san yadda aka yi aka goga masa kashin kaji sai a tura karen farauta ya kamo shi.
Don haka mu dai mun ce maraba da guguwar canji, gaba-gaba dai gwamnatin adalci, gaba dai gaba dai shugabanni nagartattu abin koyi. Mun goyi baya mun amince wa sabon canji na adalci, mu ma mun yarda mun amince a sallami cin hanci da rashawa. Don haka mun yi marhabin, mun yarda da yawunmu da sa hannunmu (mu talakawa).
Mun ga yadda kungiyoyin matasa suka yi cincirindo a fadar Shugaban kasa ranar Litinin 17-8-2015 don nuna goyon baya ga shirinsa na sallamar cin hanci da rashawa daga Najeriya.
Ya Allah Ka yi masa jagora, amin.