Mun samar da aikin yi ga mutum 10,000 a shekara uku – Habu Fagge
Sakataren Zartarwa na Hukumar Jagoranci da Shawarwari ta Jihar Kano, Alhaji Habu Ibrahim Fagge ya ce daga cikin ayyukan da hukumarsu ta aiwatar a shekara uku da suka gabata, har da samar da guraben ayyukan yi dubu tara ga matasa ’yan asalin jihar da suka kammala karatu.Alhaji Habu Fagge ya bayyana haka ne lokacin da […]
Sakataren Zartarwa na Hukumar Jagoranci da Shawarwari ta Jihar Kano, Alhaji Habu Ibrahim Fagge ya ce daga cikin ayyukan da hukumarsu ta aiwatar a shekara uku da suka gabata, har da samar da guraben ayyukan yi dubu tara ga matasa ’yan asalin jihar da suka kammala karatu.
Alhaji Habu Fagge ya bayyana haka ne lokacin da suke tattaunawa da wakilinmu a Kano, inda ya ce kimanin ayyukan da suka samar guda 4,000 sun samar da su ne a hukumomin Gwamnatin Tarayya da na jiha da suka hada da aikin soja da dan sanda da na hukumar kwastam da sauransu, sai sauran gurabe 5,000 a kamfanoni da wurare masu zaman kansu.
Ya ce, “Mu muke zuwa ko mu tura jami’anmu su je cibiyoyin daukar aikin masu damara, domin mu tabbatar an dauki yawan ’yan asalin Jihar Kano gwargwadon kason da aka ware wa jihar a tarayya.”
Ya ce hukumar tana mayar da hankali tare da sa ido don ganin cewa kason jihar na ayyuka da gurabe a ma’aikatun tarayya, an cike su da ’yan asalin jihar, kamar yadda tsarin raba daidai ya tanada a kasar nan.
Alhaji Habu Fagge ya ce hukumarsu ce take ba daliban makarantun sakandire jagoranci da fadakarwa game da karatun da ya dace da su da kuma irin sana’ar da za su yi a nan gaba. Ya ce “Aikinmu ne mu bayar da shawara da jagoranci ga duk wani dan jihar nan da yake bukatar nusarwa, ba btare da mun karbi ko kwabo a wajensa ba, domin gwamnatin jiha ce take biyanmu kuma ita muke yi wa aiki.”
Ya ce akwai fannin ba da jagoranci da fadakarwa a hukumar ilimi ta jiha da kuma makarantun sakandire don gudanar da wannan aiki na bayar da jagoranci ga dalibai masu tasowa. Sai dai kuma ya koka da ganin cewa har yanzu iyaye da dama ba su damu da halin karatun ’ya’yansu ke ciki ba, balle su nemi a nusar da su nau’in hanyar kwarewar da za su dauka tun suna yara ba.f