Mun sami rahoton aikata fyade sau 652 a shekara biyu – Cibiya
Daga cikin wadanda aka yi wa fyaden har da mai shekara daya da rabi.
A cikin tsawon shekara biyu da kafa Cibiyar Kula da Wadanda aka yi musu fyade da ke da mazauni a Asibitin Hajiya Gambo Sawaba a Kofar Gayan, Zariya, cibiyar ta kula da yara 652 da aka yi wa fyade, cikinsu har da ’yar shekara daya da rabi. Shugabar Cibiyar, Hajiya Amina Umar Faruk Ladan ta bayyana haka a ya yin tattaunawarta da
Aminiya: Yaushe aka kafa wannan cibiya?
An kafa wannan cibiya ce a ranar 7 ga Fabrairun shekarar 2019, kuma Gwamnatin Jihar Kaduna a karkashin Gwamna Nasiru El-Rufa’i, ta samar da ita, an kuma samar da irinta a wurare hudu na jihar.
- Mahara sun kashe mutum 30 a Kudancin Kaduna
- Dakarun Nijar sun ceci sojojin Najeriya daga harin ’yan bindiga
Daya a garin Kafanchan sai biyu a cikin garin Kaduna, wato Asibitin Gwamna Awan da Asibiti Dan Tsoho, sai kuma wannan ta Asibitin Hajiya Gambo Sawaba da ke Kofar Gayan, Zariya. Ita tamu cibiyar tana kula ne da Shiyya ta Daya da ta kunshi kananan hukumomi takwas.
Dalilin kafa wadannan cibiyoyi shi ne a sa ido domin tantance wadanda aka ci zarafinsu maza da mata ta hanyar yi musu fyade, domin ba su kula da taimakon duk da ya kamata da kuma dakile yawaitar aikata cin zarafin da fyaden.
Ta wace hanya kuke samun bayananku?
Da farko mun zagaya kananan hukumomi mun zauna da shugabannin al’umma da na addini da kuma jami’an tsaro da ’yan sa-kai, mun fadakar da su tare da nuna musu illar kyale masu aikata irin wannan mummunan laifi. Don haka, muna samun hadin kansu sosai wani lokaci masu unguwanin ne suke turowa mana ko jami’an tsaro ko kuma su iyayen ne da kansu suke kawo kukansu.
Daga lokacin da aka kafa cibiyar zuwa yanzu mutane nawa kuka duba?
To daga lokacin zuwa yanzu mun kula da wadanda aka ci zarafinsu ta hanyar fyade, har yara maza da mata 652, sai dai matsalar ita ce ba za mu iya tabbatar da cewa an yi musu hukunci ba, illa kadan daga cikinsu, saboda yadda iyaye ke kin ba mu hadin kai, ta hanyar ba mu bayanan karya na adireshin gida ko lambar waya, saboda gudun fallasa. Wane nau’in cin zarafin fyade kuka fi samu? Kusan duk irin nau’in muna samu na yara maza da aka yi wa luwadi da yara mata da aka bata su. Kuma a gaskiya duk yawanci matsalar fyaden daga kwaryar cikin garin Zariya muke samu. Domin kashi 70 daga cikin 100 duk a nan ne, sai kashi 30 daga sauran kananan hukumomi.
’Yan shekara nawa aka fi samu?
An fi samun ’yan kasa da shekara17, kuma mafi yawan wadanda suka haura shekara 18 za ka ga suna da lalurar tabin hankali musamman maza.
Idan kuma mata ne za ka ga cewa a gida ne aka aikata hakan. Misali, kawun yarinya ko kanin mahaifi. Yara mata masu irin wadannan shekaru tursasa su ake yi domin wani lokaci har da shigar ciki suke zuwa mana.
Akwai wata yarinya ’yar shekara 13 tana makarantar firamare ne kanin mahaifiyarta ya ci zarafinta har ma ciki ya shiga yanzu haka maganar da muke yi da kai, ta haihu muna shirin yadda za ta koma makaranta.
Wane kalubale kuke fuskanta?
Kalubalen da muke fuskanta bai wuce na matsalar iyayen yaran da lamarin ya faru da su ba.
Domin mu aikinmu ba wai kawai ya tsaya a kan duba lafiya ne ko ba su magani ba, a’a har da bin diddigin ganin an kamo wanda ya ci zarafin don ya fuskanci hukunci. To amma sai dai iyayen ba sa son haka saboda wai gudun fallasa.
Sai dai mu idan aka zo mana da matsalar cin zarafin yara kuma babu wani jami’in tsaro ba ma yarda, sai mun kira su, domin su shigo ciki saboda a gano kuma a kamo wanda ya aikata hakan a binciki lafiyarsa ko yana dauke da wata cuta domin daukar mataki da kuma gabatar da shi a kotu.
Daga cikin matsalolin fyade da kuka samu wanne ne ya fi tsaya miki a rai?
Gaskiya wanda ya fi ba ni al’ajabi da tausayi da ban haushi shi ne na wata yarinya da aka kawo ’yar shekara daya da rabi wadda mahaifiyarta ta kai ta Kano yaye, to a can ne aka yi mata fyade aka bata ta. Da ta kawo ta nan muka duba mu ka ga irin barnar da aka yi wa yarinyar sai muka hau yi mata tambayoyi. Sai ta hau mu da fada cewa ita ba abin da ya kawo ta ke nan ba, ita kawai a ba ta magani ne ta wuce kuma abin haushi, mijinta bai ce komai ba.
Sai kuma na wani yaro dan shekara goma da wani ya bata shi da luwadi, saboda wanda ya lalata yaron iyayensa masu kudi ne, to ba sa son a yi shari’a sai suka ba mahaifin yaron kudi da kuma danginsa. Kuma suka ba mahaifiyar yaron Naira dubu 200, ta ki karba. Sai danginta da na mijin suka tarar mata don ta ki karbar kudin. Ita bukatarta a fitar wa danta hakkinsa, yanzu haka maganar tana kotu tunda ita uwar ta jajirce ta ki yarda. Uban yaron ya kaurace mata kuma ya ce idan ba ta bar maganar ba, a bakin aurenta. Ka ga wannan talauci ne ya haifar da haka, don haka gwamnati ta sa ido a kuma rika taimaka wa marasa karfi.
A kwanan baya Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta samar da dokar dandaka ga duk wanda aka kama ya aikata fyade yaya kike kallon dokar?
Na ji na kuma gani, sai dai ita maganar dandaka ai ba za ta magance matsalar ba, domin idan ka dandake mutum ai sha’awa tana nan. Dandaka ba ta dauke sha’awa, don haka a ganina duk wanda aka kama a zartar masa da horo mai tsanani wanda hakan zai sa shi nadama.
A karshe mece ce shawararki?
Shawarata ita ce mu iyaye mu lura da ’ya’yanmu in sun fita, ina suka je idan sun dawo daga ina suke? Sai kuma maganar shayeshaye abar dubawa ce, domin tana daya daga cikin abubuwan da suke haifar da duk wani mummunan laifi. Kuma jami’an tsaro, ’yan sanda da na farin kaya da ’yan sa-kai da shugabanni, a sa ido sosai. Su kuma masu shari’a su ji tsoron Allah, idan aka kawo shari’ar cin zarafi kada su yi wasa da ita a zartar da hukunci mai tsanani domin wadansu su gani don su shiga taitayinsu.