Mun samu cigaba amma akwai sauran aiki – UNOCHA

Najeriya ta samu cigaba wajen magance matsalar matsananciyar rayuwa da ta dabaibaye yankin Arewa maso Gabas, amma akwai sauran aiki a gaba. Wannan shi ne takaitaccen jawabin da ya fito daga ofishin kula da ayyukan jinkai na Majalisar dinkin Duniya. A rahoton, an nuna cewa, idan aka samar da tsari mai kyau da hadin gwiwar […]

Mun samu cigaba amma akwai sauran aiki – UNOCHA

Najeriya ta samu cigaba wajen magance matsalar matsananciyar rayuwa da ta dabaibaye yankin Arewa maso Gabas, amma akwai sauran aiki a gaba. Wannan shi ne takaitaccen jawabin da ya fito daga ofishin kula da ayyukan jinkai na Majalisar dinkin Duniya. A rahoton, an nuna cewa, idan aka samar da tsari mai kyau da hadin gwiwar sojoji, masu ayyukan jinkai za su shiga lungu da sako da ba sa iya shiga a da. “Masu ayyukan jinkai sun gamsu cewa ana samun ci gaba a bangaren kula da abinci mai inganci, musamman bayan an samu tallafi na abinci mai gina jiki na gaggawa, wanda ya taimaka matuka tun karshen 2016,” inji rahoton.

Amma a Jihohin Borno, Adamawa da Yola, har yanzu ba a shiga kananan hukomomi guda 3 ba, sai kuma 26 da ake dan shiga, da kuma 37 da ake samun shiga yadda yakamata. Rahoton ya kara nuni da cewa dukkan garuruwan da ba a iya shiga, da wadanda ake shiga amma ba yadda yakamata ba suna Jihar Borno ne. Domin a magance matsalar rashin hanya mai kyau da rashin tsaro a hanyoyin garuruwan nan, an yanke shawarar amfani da jirgin sama domin isar da kayan jinkai zuwa garuruwan, sannan kuma manyan kayan za a kai su ta kasa ne tare da rakiyar jam’an tsaro. Ana sa ran a karshen damina, za a samu damar shiga kowane bangare. Rahoton ya kuma nuna cewa akwai matsalolin tsaro a hanyar, domin akwai bama-bamai da aka binne a kasa da tsoron yin kwantan bauna, kuma wannan matsalar tana cikin abubuwan da ke kawo cikas wajen kai kayan jinkai cikin garuruwan.

UNOCHA ta lura da cewa rashin cika alkawari kamar yadda masu bayar da tallafin suka yi don magance matsalolin da suka dabaibaye yankin Arewa maso Gabas, ya taimaka wajen samun tsaiko. “A daidai lokacin da aikin tallafin na bana ya kusa zuwa karshe, ana bukatar karin tallafi domin a tabbatar an cika abin da aka tsara a tsarin ayyukan jinkai na 2017. Rahoton ya ce “Wasu bangarori da ke da muhimmanci wajen sake tsugunar da mutane, bangaren fafado da yankin kamar kiwon lafiya, ilimi yana fuskantar rashin tallafi matuka, domin an samu kashi 12 da 12 da kashi 5 ne kacal a watan Satumba.

Sannan ya kara da cewa “Ci gaban da aka samu musamman a bangaren magance matsalar rashin abinci mai gina jiki (SAM) da ya yi tsanani, wanda ke fuskantar matsala saboda rashin samun kula musamman a sabbin garuruwa da ake shiga yanzu. Rashin damar shiga wasu garuruwa ya kawo cikas  wajen samar da tallafin ga wadanda suke bukatar tallafin. Tallafin abinci ya takaita ne kawai a wasu bangarorin da masu aikin jinkan za su iya shiga kuma akwai asibitoci.” 

Kamar yadda rahoton ya nuna, kimanin Dala miliyan 6.5 ake bukata wajen gabatar da ayyuka guda biyar, da kuma magance matsalar rashin abinci mai gina jiki a garuruwan da abin ya shafa.

Amma duk da wadannan matsalolin, kusan mutum miliyan 2 suna karbar tallafin abinci ta hanyar karbar abinci ko kuma kudin abincin a duk wata. “Masu karbar tallafin abinci sun kai kimanin dubu 500 wadanda suka hada da kananan yara, mata masu ciki da mata masu shayarwa a wannan shekarar ta hanyar tsarin tallafin abinci. Ana sa ran a shekarar 2017/2018, za a mayar da hankali ne wajen ceto mutane, kare rayuwar mutane, fadada ayyuna jinkai, da kuma samar da cigaba mai dorewa.” Wadannan ayyukan tallafin za su yi kyau sosai, musamman ganin yadda ake tunanin wasu mutanen da dama za su dawo gidajensu.