Mun samu Dala miliyan daya a gidan Badeh – EFCC ga Kotu
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta shaida wa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a jiya Alhamis cewa jami’anta sun samu Dala miliyan daya (kimanin Naira miliyan 300) a dakin kwanan tsohon Babban Hafsan Tsaro Iya Mashal Aled Badeh.Hukumar EFCC ta yi zargin cewa tsohon Babban Hafsan Tsaron ya sayi gidan […]
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta shaida wa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a jiya Alhamis cewa jami’anta sun samu Dala miliyan daya (kimanin Naira miliyan 300) a dakin kwanan tsohon Babban Hafsan Tsaro Iya Mashal Aled Badeh.
Hukumar EFCC ta yi zargin cewa tsohon Babban Hafsan Tsaron ya sayi gidan da aka samu wannan kudi ne a kan Naira biliyan daya da miliyan 100 da kuma kudin da ake zargin an sace su ne daga asusun Rundunar Sojin Sama ta Najeriya a shekarar 2013. Wannan yana daga cikin bayanan da Hukumar EFCC ta gabatar a gaban Alkalin Babbar Kotun Tarayya Mai shari’a Okon Abang a jiya Alhamis lokacin da aka ci gaba da sauraren bukatar belin Mista Badeh.
Lauyan Hukumar EFCC, Mista Rotimi Jacobs (SAN) da ya gabatar da bayanin ya ce duk da Mista Badeh ya musanta mallakar gidan, an samu kayayyakinsa ciki har da hotunansa a lokacin da jami’an hukumar suka kai mamaya a cikinsa.
Hukumar ta gurfanar da Mashal Badeh a gaban alkalin Mai shari’a Okon Abang a ranar Litinin da ta gabata bisa zarginsa da aikata laifuffuka 10 da suka shafi almundahana da cin hanci da rashawa da suka kai na Naira biliyan uku da miliyan 970 mallakar Rundunar Sojin Saman Najeriya.
A ranar Litinin da ta gabata ce Mai shari’a Abang ya tura Mashal Badeh zaman jiran shari’a a kurkuku jim kadan da gurfanar da shi da kuma kamfanin Iyalikam Nigeria Limited a gaban kotunsa ka almundahana, inda ya ajiye jiya Alhamis don fara sauraren belinsa.
Sai dai jami’an kurkuku ba su kawo Badeh kotun ba a jiya, kuma daga baya alkalin ya ce za a iya ci gaba da sauraren karar kamar yadda yake a karkashin sashi na 266 na gudanar da shari’ar manyan laifuffuka tunda dai zaman na sauraron wata bukata ce.
Lauyan na EFCC ya bukaci kotun da kada ta bayar da beli ga Badeh wanda ake zargi da aikata wannan almundahana a lokacin da yake Babban Hafsan Sojin Sama.
Ana tuhumar Badeh da kashe Naira miliyan 878 na sojin saman Najeriya wajen gina wa kansa wani rukunin shaguna a Abuja, kuma ana zarginsa da karkatar da kudin sojin sama wajen sayen wasu zababbun kadarori a Abuja.
Takardar karar ta ce: “Kai Iya Cif Mashal Aled S. Badeh (kasancewarka shugaban sojin sama) da kamfanin Iyalikam Nigeria Limited a tsakanin watan Janairu da Disamban shekarar 2013 a Abuja da ke karkashin hurumin wannan kotu, kun yi amfani da Dala da take daidai da Naira biliyan daya da miliyan 100, da kuka cire daga asusun sojin sama don saya wa kanku wani gidan kasaita a Lamba 6 Titin Ogun Riber daura da Titin Danube da ke Maitama, Abuja, alhali kuna sane cewa wannan kudi an fitar da su ne ta haramtacciyar hanya (cin amana da almundahana) daga Iya Cif Mashal Aled S. Badeh, kuma yin hakan aikata laifi ne da ya saba wa sashi na 15 (2) (d) na dokar yaki da yi wa tattalin arziki zagon kasa ta shekarar 2011 da za a iya hukunta ku a karkashin sashi na 15 (3) na wannan doka.”
Sauran tuhumce-tuhumce da ake yi wa Mashal Badeh sun hada da yin amfani da Dala da suka kai Naira miliyan 650 da ya cire daga asusun Rundunar Sojin Najeriya domin saya wa kansa wani fili a fuloti mai lamba 1386 a Oda Crescent, Cadastral Zone A07, Wuse II, Abuja, duk da ya san cewa wannan kudi haramun ne a taba su ta irin wannan hanya.
Ana kuma zargin Aled Badeh, da yin amfani da Naira miliyan 400 wajen saya da gyawa wani gida a Lamba 19 Kumasi Crescent, Wuse II, Abuja da aka ce ya sa wa dansa Aled Badeh Jr.
Sai dai Mashal Badeh wanda ya je kotun sanye da kaftani mai ruwan kasa da ya musanta zarge-zargen.