Mun samu nasara ne saboda kyawawan manufofinmu -Kodinetan kungiyar Arewa United
kungiyar hada kan ’yan Arewa da ke zaune a Jihar Legas (Arewa United Consultatibe Forum) ta ce kyawawan manufofinta ne ya sa mutane da dama suke son hada kai da ita.Babban kwadinetan kungiyar na kasa, Alhaji Ado Shu’aibu dansudu, wanda ya bayyana haka yayin da yake tattaunawa da Aminiya, a karshen makon da ya gabata, […]
kungiyar hada kan ’yan Arewa da ke zaune a Jihar Legas (Arewa United Consultatibe Forum) ta ce kyawawan manufofinta ne ya sa mutane da dama suke son hada kai da ita.
Babban kwadinetan kungiyar na kasa, Alhaji Ado Shu’aibu dansudu, wanda ya bayyana haka yayin da yake tattaunawa da Aminiya, a karshen makon da ya gabata, ya ce kungiyar ta sami nasarori masu yawa. “Ci-gaba da muka samu na farko dai shi ne kyawawan manufofin kungiyarmu da kuma alkiblar da ta fuskanta, ya sa mutane da yawa, ba ’yan Najeriya ba kawai, har da mutanen kasashen waje suna neman mu hadu da su mu tattaunawa wasu abubuwa da za su ciyar da kasar mu gaba da kuma matsalolin da suke damun Arewacin Najeriya. Mun tattauna da karamin jakadan Amurka mai kula da ’yancin dan Adam da siyasa, Mista Ben Lazarus da jakadan Faransa.
“Bayan haka mun tattauna da Dokta Aled Akinyele da Dokta Fredrik Fasheun da Gani Adams da gwamnan Jihar Legas da kwamishinoninsa da sauran muhimman mutane dangane da matsalolin da suka shafi ’yan Arewa da ke zaune a Legas”. Inji shi.
Alhaji Ado ya ce tattaunawar da suka yi da karamin jakadan Amurka ta sami nasara kuma sun fahimci juna, inda karamin jakadan ya ba da tabbacin zai duba abin da suka gaya masa tare da tura lamarin ga gwamnatin Amurka don daukar matakin da ya dace.
Ya kara da cewa tattauwarsu da gwamnatin Jihar Legas ita ma ta sami nasara mai yawa, inda ya ce, “Gwamnati ta yi mana alkawarin hana karbar haraji da ake yi a hanyoyin Legas daga mutanen Arewa masu shigo da kayayyaki da kama ’yan Arewa da ake yi a Legas ba gaira ba dalili”.