Mun samu nasarar gudanar da taron mawakan Hausa na duniya a Bauchi
Alhaji Haruna Aliyu Ningi, shi ne Shugaban kungiyar Mawaka ta kasa Reshen Jihar Bauchi. A kwanakin baya ne aka gudanar da babban taro na kungiyar mawakan a Bauchi, inda a cikin tattaunawarsa da wakilinmu ya yi fashin baki game da yadda aka gudanar da taron, sannan kuma ya bayyana matakan da gwamnatin jihar ta fara […]
Alhaji Haruna Aliyu Ningi, shi ne Shugaban kungiyar Mawaka ta kasa Reshen Jihar Bauchi. A kwanakin baya ne aka gudanar da babban taro na kungiyar mawakan a Bauchi, inda a cikin tattaunawarsa da wakilinmu ya yi fashin baki game da yadda aka gudanar da taron, sannan kuma ya bayyana matakan da gwamnatin jihar ta fara dauka na kirkiro da Hukumar Tace Fina-finai da Wakoki. Ga yadda tattaunawar ta kasance kamar haka:
Da farko, ko wane ne Haruna Aliyu Ningi?
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukacin Sarki, sunana Alhaji Haruna Aliyu Ningi, Shugaban kungiyar Mawakan Jihar Bauchi kuma mun kafa wannan kungiya ce domin ganin mun kawo sauyi game da yadda ake gudanar da fina-finai da wakoki a Jihar Bauchi da ma Najeriya baki daya.
Ina daya daga cikin wadanda suka ba da gagarumar gudunmawa wajen waka ga tsohuwar jam’iyyata ta PDP amma yanzu mun yi hannun riga. Wannan kungiya tana da dimbin mambobi a Bauchi, daga ciki akwai mata da matasa; kowa da yadda yake gudanar da wakokinsa.
Me za ka ce game da yadda aka kammala taron mawaka na duniya a Bauchi?
Kamar yadda kowa ya sani ne, an gudanar da taron mawaka na duniya a Bauchi, mun samu sama da mawaka 300; wadanda suka fito daga jihohi daban-daban. Akwai ma wadanda suka zo daga kasashen waje. Wannan taro, an dauki tsawo kwanaki uku ana gudanarwa.
Matar Gwamnan Jihar Bauchi, Hajiya Hadiza Muhammad Abubakar da matar Shugabar Majalisar Dokokin jiha da matar mataimakin gwamna, dukkansu sun halarci wajen taron kuma sun gabatar da jawabai daya bayan daya. Sun bayyana cewa mawaka suna daga cikin jerin mutanen da suke ba da gagarumar gudunmawa wajen hada kan al’umma, don haka gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa mawaka ta kowace fuska.
Akwai wasu matsaloli da kuka fuskanta a lokacin gudanar da taron na duniya?
Gaskiya babu wata matsala da muka fuskanta a lokacin gudanar da taron. Hukumomin tsaro sun ba da gudunmawa wajen caje dukkan wanda zai shiga dakin taron, sannan kuma mun raba katin shaida ga wadanda suka fito daga kasashen Nijar, Chadi, Kamaru, Benin, Ghana da makamantansu. Kuma ya kamata al’umma su fahimci cewa wannan taro ya haifar da dimbin alheri a Jihar Bauchi, ’yan kasuwa sun samu ciniki da walwala da sauran ’yan acaba da masu tuka Keke Napep, domin baki sun yi yawa a garin. Duk inda ka fito sai ka hadu da dimbin mutane wadanda suka fito daga wajen taron. Tabbas, akwai wadanda suke munanan kalamai ga mawaka da masu shirya fina-finan Hausa, muna ba da shawarwari ga al’umma. Idan mutum ba zai fadi alheri ba a kan mawaka to don Allah Ya yi shiru.
Tun lokacin da ka fara waka ka yi wakoki sun kai nawa?
Gaskiya ba zan iya tuna adadin wakokin da na yi a duniya ba, domin ba na rubuta adadinsu. A kowane mako zan rera waka daya kuma na fara waka tun a shekara ta 1979. ita waka baiwa ce, ba a koyar da ita.
Mene ne sakonka ga daukacin mawakan Najeriya?
Babban sakona ga daukacin mawakan Najeriya shi ne, don Allah mu ci gaba da hada kanmu waje daya domin babu al’ummar da za ta samu ci gaba sai da hadin kai. Sannan kuma idan mutum zai rera waka, ya rika yin amfani da kalmomin da zai ja hankalin al’umma baki daya. Wannan shi ne abin da zan fada.
Da gaske ne Gwamnatin Jihar Bauchi ta ba ka kyautar mota?
Tabbas, Gwamnan Jihar Bauchi, Barista Muhammad ya ba ni kyautar mota a lokacin da muka kai masa ziyara a gidan gwamnati kuma dama ya yi mini alkawari tun a lokutan baya.
Akwai wata shawara da za ka ba ’yan mata mawaka?
Babban sakona ga ’yan mata mawaka shi ne, don Allah duk wadda ta samu miji ta yi aure, domin aure shi ne abin da ya dace da mace. Duk inda mace ta kai da rangwada da jiji da kai, matukar ba ta da miji to tana aikin banza ne a rayuwa.
Kuma yanzu haka babbar matsalar da kungiyarmu take fuskanta ita ce masu satar fasaha, sannan kuma ba mu da wata hukuma a Bauchi wadda take kula da mawaka da masu hada fina-finai amma muna godiya ga Gwamnan Bauchi, Barista Muhammad Abubakar, ya yi mana alkawarin cewa nan da kwanaki kadan zai kafa mana hukumar da za ta rika kula da tace fina-finai da wakoki. Nan take gwamna ya yi mana alkawarin kirkiro da wannan hukuma, kamar yadda Gwamnatin Jihar Kano ta kafa. Jihohi da dama suna da hukumomin da suke kula da tace fina-finai da wakoki, idan aka kafa hukumar za ta dauki sabbin ma’aikata sannan kuma Gwamnatin Bauchi za ta samu kudaden shiga masu dimbin yawa. Matsalar da mawaka da masu hada fina-finai suke fuskanta ita ce satar fasaha.
Mene ne sakonka ga wadanda suka halarci taron Bauchi?
Ina mika sakona ga Wamban Kano, Alhaji Aminu Ado Bayaro da Sarkin Bauchi, Alhaji Dokta Rulwanu Suleiman Adamu da sauran sarakunan gargajiya da masu unguwanni; wadanda suka halarci taron. Allah Ya saka wa kowa da alheri.
Game da kafafen watsa labarai fa, me za ka ce a kansu?
Jaridar Aminiya tana daya daga cikin jaridun da suka ba da gagarumin gudunmawa wajen bunkasa harshen Hausa kuma ina tabbatar maka da cewa nan da watanni uku zan rera wata sabuwar waka ga Aminiya, wadda ina fatar gidan rediyon Faransa za su rika sa wa a ranar Juma’a da safe. Yanzu haka shirye-shirye sun yi nisa wajen rera wakar, domin akwai lokacin da na yi waka ga Alhaji Kawu Sumaila, na ambaci Aminiya a cikin wakar. Da ya saurara sai ya ce min dama kana karanta Aminiya? Sai na ce masa tabbas ni da Aminiya mutu ka raba.
Masu cin abinci ta sanadiyar waka suna da yawa, akwai masu sutudiyo akwai masu kaset, akwai masu sayarwa a shaguna. Zaben shekarar 2015, mawaka suna daga cikin wadanda suka ba da gudunmwa wajen sukar PDP da magoya bayanta. Don haka lokacin zabe talakawa suka zabi abin da suke bukata, mu muka tallata PDP a baya daga bisani muka kwance mata zani a tsakiyar kasuwa.
Daga karshe mene ne sakonka?
Babban sakona shi ne, ina ba da shawara ga al’umma mu ci gaba da addu’a ga sabbin shugabannin da aka zaba. Na biyu matasa don Allah kowa ya nemi wata sana’a wacce zai rika yi, domin zaman kashe wando ba zai haifar da alheri ba ga matasan Najeriya. Sannan kada mutum ya bari wasu su yi amfani da shi wajen tada zaune tsaye a tsakanin al’umma.