Mun samu nasarar kai Hukumar Kwastam zuwa babban matsayi – Hameed Ali

Shugaban Hukumar Kwastam ta kasa, Kanar Hameed Ali ya ce Hukumar Kwastan ta samu nasarar hawa babban matsayi, ta fuskar tsare-tsaren da aka samar a hukumar masu cike da kalubale, kuma ana ci gaba da samun nasara.  Hameed Ali wanda ya bayyana haka a yayin da yake jawabi lokacin bikin yaye daliban Kwalejin Ma’aikatan Hukumar […]

Mun samu nasarar kai Hukumar Kwastam zuwa babban matsayi – Hameed Ali
Mun samu nasarar kai Hukumar Kwastam zuwa babban matsayi – Hameed Ali

Shugaban Hukumar Kwastam ta kasa, Kanar Hameed Ali ya ce Hukumar Kwastan ta samu nasarar hawa babban matsayi, ta fuskar tsare-tsaren da aka samar a hukumar masu cike da kalubale, kuma ana ci gaba da samun nasara. 

Hameed Ali wanda ya bayyana haka a yayin da yake jawabi lokacin bikin yaye daliban Kwalejin Ma’aikatan Hukumar da ke Abuja, ya kara da cewa daga cikin nauyi uku da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya dora masa, na sake fasalin hukumar da samar da tsarin tara wa gwamnati haraji, ayyuka ne masu tattare da kalubale. 

Ya ci gaba da cewa, kasar nan ta fara cin moriyar wasu tsare-tsaren da aka kaddamar da su, sai dai har yanzu akwai wasu jami’an hukumar da ba su rungumi tsare-tsaren ba. Da ya juwa ga daliban da aka yayen su 40, ya shawarce su da su yi amfani da horon da suka samu a kwalejin don zamowa jakadun canji na hukumar a dukan fannoninta.

Ya kara da cewa “A yau mun samu nasarar kai hukumar zuwa matsayi babba, domin kuwa mutane suna girmama jami’anta da kuma fara samar da canji a hukumar a kan yadda take gudanar da ayyukanta. Ba ma tambayar a ba mu cin hanci sai dai wadansu na ci gaba da yin haka, amma a wurare kalilan suke iya yin haka.” 

Daga cikin dalibai 40 da aka yaye, tara mata ne. A jawabinsa tunda farko, Shugaban Kwalejin, Eporwei Edike ya ce, kwalejin za ta ci gaba da yaye dalibai masu hazaka da za su samar da canji a kan tsare-tsaren da hukumar take yi.