‘Mun samu rufin asari da a sayar da masara ‘
Wadansu masu gasa masara a birnin Abuja da suka danne girman kai, suna gasa masara, sun ce sun ci sun sha a cikin wannan harkar. A duk ranar duniya ko da rani ko kuma da damina ana sayar da gasasshen masara a Unguwar Wuye kusa da rukunin gidajen ma’aikatar kudi da ke daura da […]
Wadansu masu gasa masara a birnin Abuja da suka danne girman kai, suna gasa masara, sun ce sun ci sun sha a cikin wannan harkar.
A duk ranar duniya ko da rani ko kuma da damina ana sayar da gasasshen masara a Unguwar Wuye kusa da rukunin gidajen ma’aikatar kudi da ke daura da Zone Seben, Wuse, da ke birnin Abuja, idan mutum ya wuce Shatale-talen Berger, inda ya nufi Babban Asibitin kasa. Wadannan bayin Allah suna sawowa, gasawa, da sayar da masara shekaru da dama.
daya daga cikinsu, Ahmadu Tijjani Kusada ya shaida wa Aminiya cewa, bayan da ya yi wa Abuja tsinke, sai ya fara sana’ar sayar da Lemu da Ayaba a tsakiyar birnin Abuja kusa da gidan Tofa, amma sai ya koma sayar da gasasshiyar masara, inda ya shafe shekaru goma yana wannan sana’a.
Ya kara da cewa yana samo masarar da suke sayarwa ne da rani daga garuruwan Gada-Biyu kusa da Garin Abaji, da kasuwar garin Masaka, da garin Dikko da ke Suleja ta Jihar Neja da kuma garin Sabon Wuse da ke Jihar Neja kan hanyar Kaduna daga Abuja. A cewarsa: “Muna sayen gonar masara daga Naira dubu goma zuwa dubu hamsin, muna yin asubanci suna zuwa karyowa, gasawa da kuma sayarwa. Don ba ma sayar da wacce take ba sabuwar karya ba, wacce ba ta da laushi da zaki, shi ya sa suke samun kasuwa ba kakkautawa daga talakawa da kuma manyan mutane, har da masu jiniya don ba ma sayar da kwantai.” Ahmadu Tijjani ya ce yana gasa buhu daya da rabi don su biyu suke wurin a yanzu.
Bugu da kari, Malam Sadanu Bala Kusada ya ce, “Na kwashe shekaru goma sha biyu ina gasa masara a wannan wuri, da wannan kasuwancin na samu na yi aure, ina da d daya, ina taimakon iyayena, na gina gida, na sayi gona babba, da kuma feguna guda biyu. Amma saboda zafi, ina shirin sauya sana’ar don in koma sayar da kayan mata ‘yan kanti.”
Sun kara da cewa sun ji dadin yadda wata babbar ma’aikaciya da sauran mutane suka tsawata wa masu kama su da zargin cewa suna yin sana’a ba a inda ya dace ba, ta ce ba a barin datti a wurin, don haka a bar mu.
Wani abin mamaki shi ne yadda masu kwakwa da ke talla don wasu na sayen kwakwan su hada da masara su ci, kamar yadda Abdulkarim Kano mai kwakwa ya ce kasuwa tana yin kwayo domin ana kare samun masu saye don hadawa da masara su ci.
Sun ce sana’ar na da riba sai dai suna fama da zafin wuta.
Ahmadu Tijjani ya ce ya yi aure, ya gina gida, yana da kuma da ’ya’ya uku. “Abin mamaki shi ne duk mai sayar da masarar yana da ma’aikaci da yake sayar masa, don in ba haka ba, kafin ya kunshe ya mika ya karbo kudi ga masu saye a cikin mota ya dawo, sauran masarar aka sa a wuta zai ‘kone. Abdulrashidu Daura na daya daga cikin wadanda suke sayarwa da kuma koyon gashin masara daga AhmaduTijjani, in an tashi daga sana’a ana ba shi Naira dubu daya bayan an saya masa abinci ya ci da rana.