…Mun san inda ’yan matan Chibok suke – Hukumomin tsaro
Hukumomin tsaron Najeriya sun sake nanatk cewa sun san inda ake tsare da ’yan matan sakandaren Chibok su fiye da 200 da ’yan Kungiyar Boko Haram suka sace.Manyan hafsoshin tsaro ne suka shaida wa Majalisar kasa da ke ba da shawara kan harkokin mulkin kasar haka a ranar Talata inda suka ce kubutar da ’yan […]
Hukumomin tsaron Najeriya sun sake nanatk cewa sun san inda ake tsare da ’yan matan sakandaren Chibok su fiye da 200 da ’yan Kungiyar Boko Haram suka sace.
Manyan hafsoshin tsaro ne suka shaida wa Majalisar kasa da ke ba da shawara kan harkokin mulkin kasar haka a ranar Talata inda suka ce kubutar da ’yan matan na bukatar taka-tsantsan.
Jami’an tsaron sun kuma yi wa majalisar bayani kan irin kalubalen da kasar nan ke fuskanta ta fuskar tsaro.
Wannan dai ba shi ne karon farko da jami’an tsaro ke ikirarin cewa sun san inda ake boye da ’yan matan Chibok ba.
A kwanakin baya Babban Hafsan Tsaro, Iya Mashal Aled Badeh ya ce jami’an tsaro sun san inda ’yan matan suke, sai dai ya ce akwai bukatar a yi kaffa-kaffa wajen ceto su don gudun kada su hallaka.
A wani labarin kuma rundunar ’yan sandan Najeriya ta dakatar da bayar da lasisin mallakar sababbin bindigogi, har sai bayan babban zabe mai zuwa.
Umarnin na rundunar ’yan sandan, wani kandagarki ne don kauce wa amfani da bindigogi ta hanyoyin da ba su dace ba.
kwararru sun ce dokar ba za ta magance matsalar tsaro a kasar nan ba.