Mun san wanda ya kashe ’ya’yana – Zakzaky

Jagoran ’yan uwa Musulmi Sheikh Ibrahim Yakub Zakzaky ya yi zargin cewa wani hafsan soja da ke Zariya mai suna Birgediya Janar S. Okuh ne ya kashe masa ’ya’yansa uku da kuma mabiyansa fiye da talatin.Sheikh Ibrahim Zakzaky ya yi wannan zargi  ne a yayin da Mista Sam Nda Nsiah ya je don yi masa […]

Mun san wanda ya kashe ’ya’yana – Zakzaky
Mun san wanda ya kashe ’ya’yana – Zakzaky

Jagoran ’yan uwa Musulmi Sheikh Ibrahim Yakub Zakzaky ya yi zargin cewa wani hafsan soja da ke Zariya mai suna Birgediya Janar S. Okuh ne ya kashe masa ’ya’yansa uku da kuma mabiyansa fiye da talatin.
Sheikh Ibrahim Zakzaky ya yi wannan zargi  ne a yayin da Mista Sam Nda Nsiah ya je don yi masa ta’azziyya, inda ya ce wannan hafsa shi ne ya jagoranci kashe masa jama’a, ‘domin muna da shaidu da hotonan bidiyo da suke tabbatar da shi ne ya kashe mana ’ya’ya.’
Sai dai kuma Kakakin Hedkwatar Sojan Najeriya Manjo Janar Chris Kolade ya ce hukumar soja za ta yi bincike don gano duk wani mai hannu a cikin wannan kisan gilla da aka yi
Ya ce hukumar soja ta damu da wannan kisa da aka yi kuma za ta tabbatar ta yin bincike don gano asalin abin da ya furu.
Sojoji ba sa kisa haka nan kawai, “Kuna da labarin cewa mu aka fara harbi sannan muka maida martani, ku san cewa ba daidai ba ne a ce wani ya harbi soja alhalin mu ne ke tsaron lafiyar al’umma. Ba ma fada da kowa, musamman farar hula, don haka kada ku ci gaba da ba da labarin abin da zai hargitsa mutane, za mu tabbatar da mun yi binceke a kan abin da ya faru, kuma duk wanda aka sama ya yi ba daidai ba, to za mu hukunta shi, su ma za mu gano ko sun yi harbi, idan sun yi harbi to ba za mu kyale su ba, za mu dauki matakin da ya dace domin zaman lafiya,” inji shi.   
A ranar Juma’a ce takaddama da ta auku a tsakanin ’yan Shi’a magoya bayan Sheikh Ibrahim Zakzaky da sojoji a Zariya inda almajiran malamin 35 ciki har da ’ya’yansa uku suka rasa rayukansu.
Majiyarmu ta ce, rikicin ya samo asali ne a yayin da ’yan Shi’a suke gudanar da zanga-zangan Ranar kudus, kamar yadda suka saba a ranar Juma’ar karshe na watan Ramadan.
Majiyar ta ce sun yi jiren gwano suna cikin tafiya sun kai daidai kwanar gidan man Oando da ke kan titin Sakkwato Road sai rigima ta barke a tsakaninsu da wadansu sojoji inda aka harbe wadansu daga cikin mabiya Shi’ar.
Sheikh Ibrahim Zakzaky ya shaida wa wani taron manema labarai cewa, “Kamar kowace shekara mun saba gudanar da muzahara kuma mun fara abinmu lafiya mun kare lafiya domin har mun yi addu’a.” Ya ce kamar sauran jihohi a nan Najeriya an gudanar da wannan muzaharar a Kaduna da Bauchi da sauransu har da kasashen waje sun gudanar da wannan muzahara ta Ranar kudus, “Bayan mun kammala muna hayarmu ta dawowa sai kawai sojoji suka yi mana kwanton bauna a gonakin rake muna isowa suka bude mana wuta suka kashe wasu daga cikinmu suka kama wasu,” inji shi.
Sheikh Zakzaky ya kara da cewa “A cikin wadanda suka fara harbi har da dana mai suna Mahmud inda suka harbe shi a ciki, bayan mun kwashe wadanda suka harba za mu kai su asibiti, sai suka tare hanya har sai da wasu suka cika har da Mahmud, uama suka kama wasu daga cikin mutanenmu har da ’ya’yana uku; Aliyu da Hamid da Ahmad ida suka tafi da su barikinsu na Basawa da ransu, daga baya Aliyu  ya bugo min yawa cewa, Baba an kashe Ahmad da Hamid, ni kuma an harbe ni a kafa.”
Sheikh Zakzaky ya ce ya nemi wadanda ya kamata domin ya shaida musu a ba shi ’ya’yansa amma abin ya ci tura. Ya ce a lokacin da ya nemi Kwanishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna ya yi magana ko ya ba shi DPO domin ya je a ba shi gawarwakin ’ya’yansa da almajiransa da dansa da aka yi wa rauni don kai shi asibiti, sai ya ce wai kwamandan ya ce ya je asibitin Shika ya kai su can. “Na tura jama’ata da motar daukar marasa lafiya domin a kwaso su sai suka kwace motar, kuma suka dauke direban motar yanzu haka ba mu san halin da yake ciki ba, na rasa gane irin wannan al’amari sannan wai kuma an ce ana gudanar da mulkin dimokuradiyya, wannan shi ne ainihin abin da ya faru ba wai fada muka yi ba, domin mun saba gudanar da wannan muzaharar duk shekara lafiya lau saboda haka wannan shiri ne kawai aka yi domin a yake mu kuma ina ganin fada nake yi kai-tsaye da kamandan sojojin Najeriya,” inji shi.
Aminiya ta tuntubi Kakakin Sojojin Daffo da ke Zariya Laftana Hashim Abdullahi Sa’ad inda ya ce rikicin ya faru ne a yayin da da kwamandan sojojin barikin Basawa ya zo wucewa su kuma ’yan Shi’a suka hana shi, har ma wani daga cikin ’yan Shi’ar ya bude wuta a kan sojoji, su kuma sojojin ba su yi wata-wata ba wajen maida martani.
 Laftana Sa’ad ya ce za a yi bincike domin gano wanda yafara harbi daga cikin ’yan Shi’ar da sauran abubuwan da suka biyo baya.
A ranar Litinin ne aka yi jana’izar wadanda suka rasun, ciki har da ’ya’yan Sheikh Zakzaky uku; Ahmad da ke karatun kimiyyar sinadarai a Jami’ar Chenyang ta kasar China da Hameed da shi ma ke karatun injiniyan jirgin sama a Jami’ar Kimiyya ta dian da ke China da kuma Mahmud da ke karatu a Jami’ar Al-Mustapha da ke Beirut, Lebanon kuma Sheik Zakzaky ne ya jagoranci yi musu Sallah a gidansa da ke Gyellesu.