Mun sauke nauyin basussukan kamfanonin jiragen saman kasashen waje da ke kanmu – Sirika
A farkon wannan makon ne Gwamnatin Tarayya ta ce, ta samu nasarar kammala biyan basussukan da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje masu yin aiki a kasar nan ke bin ta. Minista a Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika, wanda ya bayyana biyan basussukan a mastayin daya daga cikin nasarorin da suka samu a bangaren […]
A farkon wannan makon ne Gwamnatin Tarayya ta ce, ta samu nasarar kammala biyan basussukan da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje masu yin aiki a kasar nan ke bin ta. Minista a Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika, wanda ya bayyana biyan basussukan a mastayin daya daga cikin nasarorin da suka samu a bangaren ayyukan jiragen sama, ya bayyana cewa, sun fuskanci bazaranar ficewa daga Najeriya da wasu daga cikin kamfanonin jiragen sama suka yi matukar gwamnati ta gaza biyansu kudadensu.
A cewar gwamnati, basussukan da yawansu ya kai Dala miliyan 600, a lokacin da tattalin arzikin Najeriya ya tabarbare, amma kawo yanzu gwamnatin ta biya su, duk da karancin kudin da take fuskanta a yanzu. Ta ce, jinkirin biyan basussukan ya faru ne sakamakon karancin kudi da gwamnatin ta yi fama da shi, sannan da faduwar farashin danyan man fetur a kasuwar duniya.
A watan Satumba bara ce, kamfanonin jiragen sama na kasashen waje masu yin aiki a Najeriya, suka fuskanci Gwamnatin Tarayya kan ta biya su kudaden da suke bin ta. Duk da su kansu a lokacin sun tabbatar da cewa ba Najeriya ce kadai suke bi bashi ba, sakamakon karancin kudin cinikin danyen man fetur da faduwar farashinsa a kasuwar duniya. Kamfanonin sun ce basussukan suna shafar ayyukansu, kuma a lokacin da matsalar faduwar farashin man ta tsananta, kasashe irin su Benezuwela, wacce lamarin ya fi shafa, kamfanonin sun biyo ta bashin fiye da Dala biliyan 3 da miliyan 780 sai kasar Sudan Dala miliyan 360 sai Masar Dala miliyan 291 da kuma Angola da suka bi ta bashin Dala miliyan 237.
Najeriya ta rika biyan kamfanonin kudadensu, inda zuwa watan Agustan 2017, kudin ya ragu zuwa Sala milyan 175 kacal, wanda kamar yadda kamfanonin suka ce na cinikin tikiti ne da aka yi. Ci gaban da aka samu ta fuskar biyan kudaden, ya faru ne sakamakon karin farashin danyen man fetur da aka samu a kasuwannin duniya.
Haka kuma kungiyar Masu Jiragen Sama ta Duniya (IATA), ta ce yadda aka rika biyan bashin sannu a hankali ya shafi kamfanonin jiragen kasashen waje masu yin aiki a kasar nan, wanda ta ce gaza samun kudaden nasu ne ma ya tilasta wa kamfanin safarar jiragen na Iberia da na United Airlines, suka kaurace wa harka a Najeriya baki daya.
A cikin jawabin da ya gabatar a taron masu ruwa -da-tsaki kan harkar sufurin jiragen sama da aka gudanar a kwanakin baya, Minista Sirika ya bayyana cewa kamfanonin jiragen saman suna da dalilin kokawa a kan kudaden nasu da ba a biya su ba, kamar yadda ita ma Gwamnatin Tarayya ba za ta so a rike wa nata kamfanonin kudadensu ba a waje. Ministan ya ce Najeriya ta yi duk abin da take iyawa na ganin ta biya wadannan miliyoyin dalolin ga kamfanonin. Ya ce, “A lokacin da aka bude kasuwar shinku ta musamman, da muka karbi mulki, akwai batun miliyoyin daloli da kamfanonin jiragen waje ke bin mu.
Sai muka ga hakan bai dace ba, domin ba za mu so ganin an rike wa wani kamfaninmu da yake aiki a waje kudadensa ba. Duk abin da za mu yi na ganin sun karbo kudadensu za mu yi don taimaka musu. Don haka, abin da ba za mu so a yi mana ba, ba za mu yarda mu yi wa wani kwatankwacinsa ba. Don haka ne muka tabbatar da mun biya su basussukan nasu baki daya. Kuma na san da cewa kowa ya san halin da muke ciki a wannan lokaci, ba lokaci ne da biyan wadannan makudan kudade ke da sauki a gare mu ba.” .