Mun sha alwashin bai wa Aliyu Manji kuri’unmu – kungiyoyin Matasan PDP

Hadaddiyyar Majalisar Hadaka ta kungiyoyin Matasan Jam’iyyar PDP a yankin Arewa dake karkashin kungiyar sake farfado da daraja da fasalin shugabanci a PDP ta bayyana goyon bayanta ga neman matsayin mataimakin shugaban Jam’iyyar PDP na kasa a yankin Arewa ga Alhaji Aliyu Musa Usman Manji saboda kasancewar shi ne kadai matashi daga cikin ‘yan takarar […]

Mun sha alwashin bai wa Aliyu Manji kuri’unmu – kungiyoyin Matasan PDP

Hadaddiyyar Majalisar Hadaka ta kungiyoyin Matasan Jam’iyyar PDP a yankin Arewa dake karkashin kungiyar sake farfado da daraja da fasalin shugabanci a PDP ta bayyana goyon bayanta ga neman matsayin mataimakin shugaban Jam’iyyar PDP na kasa a yankin Arewa ga Alhaji Aliyu Musa Usman Manji saboda kasancewar shi ne kadai matashi daga cikin ‘yan takarar wannan mukamin guda uku daga yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

A wani taro na masu ruwa da tsaki da ya kunshi shugabanin matasa da jagororin siyasa da wakilai na PDP a hedikwatar jam’iyyar ta kasa dake Abuja, shugabanin majalisar hadakar sun nuna amincewarsu ga baiwa matashi wannan kujerar don farfado da daraja da kimar PDP a Najeriya.

Mai Magana a madadin matasan da suka yi taron, Malam Yusuf Abubakar Aliyu ya bayyana cewar, lokaci ya yi da za a baiwa matasa dama don nuna tasu bajinta wajen fito da nasara da jagorancin jam’iyyar PDP tare da sake farfado da darajarta ga idon al’ummar kasar nan. Matasan sun bukaci wakilan da za su yi zaben sababbin shugabanin da su mayar da hankali wajen ganin an baiwa matasa dama don jagorancin PDP tare da bunkasa hadin kai, tarbiyyar aiki tare da nasara.

Shugabanin matasan daga kungiyoyi har 18 na yankin Arewa sun bayyana cewa ba-gudu-ba ja da baya ga lamarin sake tayar da komadar matsalolin PDP a yanzu, daga mummunan barci da ta yi na rashin ingantaccen shugabancin da ya janyo faduwa zabe a 2015.

“Wannan lokacin na matasa ne, ya dace wadanan iyayen namu su hakura don karfinsu ya yi rauni, tunaninsu na yan mazan jiya ba zai iya kawo mu ga nasara a wannan lokacin ba. Don haka a barwa matasa jagorancin mukamin shugabancin jam’iyya don ci gaba”

“Sakamakon matsalolin da muke fuskanta a yau, ba shakka mutane irin su Aliyu Musa Usman Manji daga Jahar Taraba da wasu matasa masu jini a jika, ke iya namijin kokari ga ceto PDP daga matsalolin da take fuskanta” Inji Malam Yusuf Aliyu.