Mun sha fitsarinmu don tsira da ranmu a hanyar Libya — ’Yar Najeriya

Matashiyar ta gargaɗi matasa da ke shirin fita ƙasashen waje neman aiki.

Mun sha fitsarinmu don tsira da ranmu a hanyar Libya — ’Yar Najeriya

Wata matashiya ’yar Najeriya mai shekaru 23, Endurance Daniel, ta bayyana irin wahalar da ta sha a tafiyarta zuwa ƙasar Libya, inda ta ce sun kai ga shan fitsari domin tsira da rayukansu a hamada saboda tsananin ƙishirwa.

Endurance, na cikin ’yan Najeriya 182 da ƙungiyar ƙasa da ƙasa kan gudun hijira ta taimaka wajen dawo da su gida.

Ta ce ta yi tafiyar tare da mutane 52 a cikin mota ɗaya, amma bakwai daga cikinsu sun rasu a hanya sakamakon yunwa, ƙishirwa da tsananin wahala.

Ta bayyana cewa an yaudare ta ne tun tana da shekaru 17, inda aka yi mata alƙawarin sama mata aiki mai kyau a Libya.

Sai dai da ta isa ƙasar, ta fahimci cewa gaskiyar rayuwa ta bambanta sosai da abin da aka faɗa mata.

“Mun shafe fiye da wata ɗaya a hamada ba tare da ruwa ba.

“A wasu lokuta muna shan fitsarinmu domin mu rayu,” in ji ta.

Ta ƙara da cewa daga baya wasu mutane har jini ke fita maimakon fitsari saboda tsananin wahala.

Ta ce wasu daga cikin abokan tafiyarsu sun rasu a hanya, kuma babu yadda za a yi da gawarwakinsu saboda tsananin yanayin da suke ciki.

Endurance ta kuma zargi masu safarar mutane da tilasta wa mata aiki ko kuma karuwanci, tare da hana su komawa gida sai sun biya kuɗin da aka kashe wajen tafiyar.

A ƙarshe, ta yi kira ga matasa da su bincika sosai kafin su yanke shawarar tafiya ƙasashen waje.