‘Mun shiga halin kunci a sakamakon kai hari garin Shani’

A ranar Asabar din da ta gabata ce wasu maharan da ake zaton ’yan kungiyar Boko Haram ne suka kaddamar da hari a yankin karamar Hukumar Shani da ke Jihar Borno, inda suka farmaki ofishin ’yan sanda da kuma gidan sarki, a yayin da kuma mazauna garin suka yi ta tserewa. Malama Fatuma Ibrahim, tana […]

‘Mun shiga halin kunci a sakamakon kai hari garin Shani’
‘Mun shiga halin kunci a sakamakon kai hari garin Shani’

A ranar Asabar din da ta gabata ce wasu maharan da ake zaton ’yan kungiyar Boko Haram ne suka kaddamar da hari a yankin karamar Hukumar Shani da ke Jihar Borno, inda suka farmaki ofishin ’yan sanda da kuma gidan sarki, a yayin da kuma mazauna garin suka yi ta tserewa.

Malama Fatuma Ibrahim, tana daya daga cikin wadanda suka tsere daga garin zuwa Maiduguri. Ta ce sun tsorata, sun kuma tsira da kyar. “Mun ji harbe-harben bindigogi a daren Asabar, shi ke nan sai muka sadakar da cewa sun shigo garinmu. Maigidana yana nan sai ya haura ta garu ya gudu ya shiga daji, ni kuma sai ya bar ni da yara. Maigidana yana gudu sai suka shigo gidanmu suka tambaye ni ina mijina, na ce masu ya yi tafiya. Sai suka ce karya kike yi, ki fito mana da shi in ba haka ba mu kashe ki. Sai na ce masu to gaskiya sai dai ku kashe ni, ni ba karya na fada maku ba, idan kuma ba ku yarda ba ne to ku duba gidan gaba daya. Shi ke nan sai suka ce to in fita ni da yarana in san inda dare ya yi mini, domin kuwa sun riga sun kwace wannan gidan. Shi ke nan sai muka fita ni da yarana hudu, muka kama hanya muna tafiya ba mu san inda za mu je ba, duk da cewar ba mu fita garin ba amma ina tunanin gidan da za mu iya shiga mu fake domin kowa yana gudu ne; yana neman mafaka, to amma mun samu wani gidan da ba a karasa ba muka shiga muka kwana. Amma akwai sanyi da sauro, kodayake ba mu iya barci ba amma mun wahala. Ga tsoro, safiya na yi sai muka kamo hanyar zuwa Maiduguri cikin tsoro da fargaba da wahala.”
Ta ci gaba da cewa: “A lokacin da muka tashi da safe, mun gan su suna kaiwa da komowa a garin kuma ni ban ga wani jami’in tsaro ko daya ba. Sun dai bar mu mun wuce amma kuma da kyar muka samu abin hawa zuwa Maiduguri. Mun dai zo Maiduguri cikin wahala da yunwa, mun kuma shiga sansanin ’yan gudun hijira, muka kuma samu wurin kwana da abinci.”
Ita ma Malama A’ishatu Hassan ta fadi cewa: “Mun tsinci kanmu a cikin wahalar da ba mu taba shiga ba, ni da yarana. Allah Ya sa mai gidana ma ba ya nan, ya yi tafiya zuwa Kaduna amma yarana sunanan kuma yawancinsu matasa ne su 6 amma Allah Ya kiyaye mu dukkanmu. Yarana duk Allah Ya ba su iko sun gudu zuwa Maiduguri, sai ni ce kawai na rage. Sun ce mana ni da wadansu mata cewa wai duk mu fita mu bar masu garin, ba su son ganin kowa a garin, amma idan muna son zama a karkashinsu to mu zauna ba za su taba mu ba amma kuma za su fara kaddamar da Shari’ar Musulunci a garin. To haka nan na hakura na zauna na kwanaki biyu kafin na samu hanya na gudu zuwa nan Maiduguri. Amma kafin in zo nan na ga irin yadda suke kashe mutane da yadda suke kone-kone, abin babu kyan gani. Na ga ba zan iya jure gani ba, shi ne na sato jiki nazo nan Maiduguri, duk da cewar babu wasu jami’an tsaro a garin. Matasan garin sun yi iya kokarinsu amma abin ya fi karfinsu, dole suka gudu. A gaskiya tun daga wancan lokacin har kawo yanzu hankalina ba shi a kwance. ina cikin damuwa domin na ga abin da ban taba gani ba kuma a yanzu haka ina cikin tsoro da figici, domin akwai tsofaffi na baro su a can, ban san abin da zai iya biyo baya ba. Ga shi kuma wasu ’yan uwan namu mun rabu ke nan, ban san inda suke ba. Kai Allah Ya kawo karshen wannan al’amarin. Ga shi yanzu ina sansanin ’yan gudun hijira a nan Maiduguri kuma muna samun abinci da wurin kwana, sai dai abin da nikan tuna in yi bakin ciki shi ne na yadda karatun yarana ya tsaya, ga shi kuma ba mu san ranar komawaba.”

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato