Mun shiga siyasa don magance rikicin ƙabilanci a Legas – Ahmad Kabir
Alhaji Ahmad Kabir, babban magatakarda na ma’aikatar kula da ruwa na Jihar Legas, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar ’yan Arewa mazauna Jihar Legas ya bayyana cewa al’ummar Arewa mazauna Jihar Legas sun shiga siyasa ne domin magance rikice-rikicen kabilanci a Kudu. A tattaunawarsa da Aminiya, dan siyasar ya bayyana cewa: “Na yi siyasa irin […]
Alhaji Ahmad Kabir, babban magatakarda na ma’aikatar kula da ruwa na Jihar Legas, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar ’yan Arewa mazauna Jihar Legas ya bayyana cewa al’ummar Arewa mazauna Jihar Legas sun shiga siyasa ne domin magance rikice-rikicen kabilanci a Kudu.
A tattaunawarsa da Aminiya, dan siyasar ya bayyana cewa: “Na yi siyasa irin ta makaranta sai kuma aka yi wani lokaci a nan cikin garin Agege an sami matsaloli na zamantakewar jama’a abin da ya shafi rigingimu na ƙabilanci tsakanin Yarbawa da Hausawan, wannan ya kashe wannan, wanccan ya kashe wannan. Nan fa muka yi amfani da shawarar da marigayi Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ya taɓa ba iyayenmu, lokacin da ya zo nan Legas ya ce su yi siyasa irin ta waɗanda suke zaune da su, domin in ka nuna kana kyamar mutum sai shi ma ya ƙi ka amma duk mutumin da ka ce kana yi da shi to zai so ka. Sai muka ga shiga cikin harkokin siyasa tare da hulɗa da shuwagabannin Yarabawa kai tsaye ne zai magance mana matsalarmu.”
Ya bayyana cewa ya zuwa yanzu, al’ummar Arewa mazauna Legas sun fara fahimtar muhimmancin hadin kai da zaman lafiya, don haka za su ci gaba da wayar da kan juna doimin ganin an ci gaba da samun zaman lafiya da hadin kan juna domin ci gaba.