Mun shirya mayar wa Amurka kowane irin martani — Iran
Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa zuwa yanzu yaƙin da ake yi da Iran bai ƙare ba.
Iran ta mayar wa Amurka martani kan sabon tayin sulhun da Washington ta gabatar, a daidai lokacin da hare-haren jirage marasa matuƙa suka sake tayar da hankali a yankin Tekun Fasha, yayin da Tehran ta yi gargaɗin cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen mayar da martani kan duk wani sabon hari daga Amurka.
Gargaɗin da Iran ta yi ya zo ne bayan da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya dage cewa yaƙin ba zai ƙare ba har sai an fitar da duk sinadarin uranium da Iran ta tace tare da rusa cibiyoyin shirinta na nukiliya.
- Kotun Ƙolin Brazil ta dakatar da dokar rage wa Bolsonaro wa’adin zaman gidan yari
- Gwamna Radda ya biya wa maniyyatan Katsina kuɗin hadaya
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa, “Ba za mu taɓa miƙa wuya ga maƙiya ba. Tattaunawa ko sulhu ba ya nufin miƙa wuya ko ja da baya ba ne.”
Kamfanin yaɗa labarai na gwamnatin Iran, IRIB, ya ce martanin Tehran da aka isar ta hannun masu shiga tsakani daga Pakistan ya fi mayar da hankali ne kan kawo ƙarshen yaƙi a dukkan fannoni, musamman a Lebanon, da kuma tabbatar da tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa.
Rahotanni sun nuna cewa tayin sulhun na Amurka ya haɗa da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin Tekun Fasha domin samar da damar tattaunawa kan rikicin da kuma shirin nukiliyar Iran.
Yaƙin bai ƙare ba — Netanyahu
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa zuwa yanzu yaƙin da ake yi da Iran bai ƙare ba har sai an kwashe sinadarin uranium da Iran ta tace tare da rusa cibiyoyin tace sinadarin.
“Har yanzu akwai sinadarin uranium da dole a fitar da shi daga Iran, sannan akwai cibiyoyin tace sinadarin da ya kamata a rusa,” in ji shi yayin wata hira da shirin “60 Minutes” na CBS.