Mun tara haraji mafi girma a tarihi a bara —FIRS
Naira tiriliyan 10.1 da aka samun ya game dukkan nau’o’i haraji da kudaden shiga aka samar.
Hukumar Tara Kudaden Shiga ta Kasa (FIRS) ta ce, ta tara harajin sama da Naira tiriliyan 10 a bara, mafi girman harajin da aka taba samu a tarihinta.
Wannan dai na kunshe ne a rahotonta na shekarar da ta gabata, wanda Shugaban Hukumar Malam Muhammad Nami ya sanya wa hannu.
- Yadda wata gobara ta gagari motocin kwana-kwana uku a Abuja
- Siyasa: An bar malaman Musulunci a baya —Sheikh Ibrahim Khalil
Bayan ganawar Nami da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, hukumar ta samu jimillar Naira tiriliyan 10 da biliyan 1, inda a fannin harkar mai hukumar ta karbi harajin Naira tiriliyan 4.09, sai kudaden shiga da ba na mai ba suka samar da Naira tiriliyan 5.96, wanda hakan ya zarta abin da aka kayyade wa hukamr na Naira tiriliyan 10.44.
Kamfanoni sun biya harajin da ya kai Naira tiriliyan 2.83; sai harajin kayyaki na musamman (BAT) da ya kai Naira tiriliyan 2.51, inda harajin canjin Kudi ta na’ura aka samu Naira biliyan 125.67 da kuma harajin da aka ware wa abubuwa na musamman da aka samu Naira biliyan 353.69.
Harajin da ba na man fetur ba da ya kai kashi 59 na adadin da abin da aka tara a shekarar, yayin da harajin mai ya kai kashi 41na yawan kudaden da aka samu,” in ji rahoton.
Rahoton ya ce, “Wannan ne karon farko da Hukumar FIRS ta taba samu harajin da ya kai Naira tiriliyan 10 a cikin tarihin kudaden shiga da take karba.”
Rahoton ya bayyana cewa, Naira tiriliyan 10.1 da aka samun ya game dukkan nau’o’i haraji da kudaden shiga aka samar ne, baya ga wasu kudaden haraji da aka bayar a karkashin dokokin tara haraji, da suka kai Naira tiriliyan 1.8.
Rahoton ya ci gaba da cewa, wannan adadi ya hada da jimillar kudaden shiga na Naira biliyan 146.27 wanda shi ne jimillar kudaden takardun shaida da hukumar ta bayar ga masu zuba jari da kuma Kamfanin Mai na Kasa don samar da ababen more rayuwa a karkashin Shirin Samar da Ababen more rayuwa.
A wata sanarwa da mataimaki na musamman a kan Harkokin Yada Labarai da Sadarwa ga Shugaban Hukumar Mista Johannes Oluwatobi Wojuola ya fitar ta ce, shugaban ya lura cewa sake fasalin hukumar da aka bullo da shi ya taimaka sosai wajen samun wannan ci gaba, wanda hakan kuma ya sa aka mai da hankali wajen zage dantse don ganin an inganta yanayin samar da haraji, ta hanyar kawar da rashin yarda da juna da kwange a karbar harajin da kuma kauce wa kin biyan haraji.
Ya ce, yin hakan ya haifar da hanyar samar da ingantaccen ilimi ga masu biyan haraji.