Mun tsere daga sel muka fara yin fashi da garkuwa- Masu laifi

Wani da ake zargin shugaban tawagar masu yin garkuwa da mutane ya ce, sun tsere daga sel din ‘yan sanda a jihar Abiya kafin su kafa tawagar yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa. Wanda ake zargin da ya fadi sunansa Anaba, wanda ayarin ‘yan sandan sirri a shiyyar Abiya suka bankado. ‘Yan sandan […]

Mun tsere daga sel muka fara yin fashi da garkuwa- Masu laifi

Wani da ake zargin shugaban tawagar masu yin garkuwa da mutane ya ce, sun tsere daga sel din ‘yan sanda a jihar Abiya kafin su kafa tawagar yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Wanda ake zargin da ya fadi sunansa Anaba, wanda ayarin ‘yan sandan sirri a shiyyar Abiya suka bankado.

‘Yan sandan sun ce, Anaba da tawagar su sun tsere daga sel din ‘yan sanda tare da sace bindigogi biyar kirar Ak47 da sauran makamai.