‘Mun tura wa EFCC $760,000 kuɗin makaranta da Yahaya Bello ya biya wa ’ya’yansa’

EFCC ta ce Yahaya Bello ya biya kuɗin ne domin karatun da ’ya’yansa za su yi a makarantar nan gaba.

‘Mun tura wa EFCC $760,000 kuɗin makaranta da Yahaya Bello ya biya wa ’ya’yansa’

Makarantar nan mai suna ‘American International School’ da ke Abuja ta ce ta tura dala $760,000 zuwa cikin asusun Hukumar Yaƙi da Rashawa (EFCC).

Kuɗin wani ɓangare na dala 845,852 da ake zargin tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya biya a makarantar domin karatun da ’ya’yansa za su yi a makarantar nan gaba.

Tun a Juma’ar da ta gabata ce dai mai magana da yawun hukumar EFCC, Dele Oyewale ya bayyana cewa makarantar ta rubuta wa hukumar takarda, cewa za ta mayar da kuɗin zuwa asusun gwamnati kasancewar hukuma na bincike a kan lamarin.

Daga bisani shugaban makarantar, Greg Hughes a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar ya ce, “sabanin rahotannin da wasu kafafen yada labarai suka bayar da ke nuna cewa har yanzu makarantar na ci gaba da riƙe da kuɗaɗen, makarantar tana bayar da tabbacin cewa ta miƙa wa EFCC wannan kuɗaɗe.”

“Dangane da miƙa waɗannan kuɗaɗen ya nuna kudurinmu na tabbatar da tsayuwa kam gaskiya da kare mutuncinmu da kuma mutunta hukumomin Najeriya.

“Bayan samun labarin cewa kuɗin makarantar da muka karɓa da wannan manufa ɗaya tilo wani ɓangare ne na shari’ar da ke gudana tsakanin Yahaya Bello da EFCC, mun miƙa waɗannan kuɗaɗen bisa ga bukatar wannan hukumar ta tarayya,” a cewar Hughes.

Sai dai Mista Hughes ya ce ba za su ce uffan ba dangane da taƙaddamar da ke tsakanin Yahaya Bello da EFCC, “saboda haka babu wani karin bayani da za mu yi a yanzu.”

Bayanai sun ce tun da farko da Hukumar EFCC ta aike wa makarantar asusun da ta sanya kuɗin a ciki, kamar yadda Mista Oyewale ya bayyana.

EFCCn dai ta yi zargin cewa tsohon gwamnan na Kogi ya cire kuɗin daga asusun gwamnatin jihar a lokacin da yake jan ragamar jihar, inda ya kai su kasuwar musayar kuɗi, don biyan kuɗin karatun ’ya’yansa har zuwa wasu shekaru masu zuwa a nan gaba.

A ranar 18 ga watan Afrilu ne dai EFCC ta ayyana neman Yahaya Bello ruwa-a-jallo, sakamakon zarginsa da ɓarnatar da kuɗaɗen gwamnatin Jihar kogi a lokacin da yake mulkin jihar.

Bayan hakan ne kuma hukumar shige da fice ta Najeriya ta fitar da wata sanarwa tana umartar jami’anta da su kama shi a duk inda suka gan shi a faɗin ƙasar.

Hukumar shige da ficen ta kuma aike da kwafin sanarwar ga rundunar ’yan sandan ƙasar da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya.

Haka shi ma babban lauyan gwamnatin ƙasar, kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya buƙaci tsohon gwamnan na Kogi ya miƙa kansa ga hukumar ta EFCC.