Mun yi alkawarin shawo kan matsalar fetur a Najeriya – Injiniyoyin Matatar Dangote
Injiniyoyin da Matatar Mai ta dangote ta tura kasar Indiya don samun horo sun yi alkawarin amfani da basirar da suka samu wajen shawo kan matsalar man fetur a Najeriya da zarar matatar ta fara aiki. Injiniyoyin wadanda suka bayyana gogewar da suka samu cewa ba ta da ta biyu a tarihin hada-hadar man fetur […]
Injiniyoyin da Matatar Mai ta dangote ta tura kasar Indiya don samun horo sun yi alkawarin amfani da basirar da suka samu wajen shawo kan matsalar man fetur a Najeriya da zarar matatar ta fara aiki.
Injiniyoyin wadanda suka bayyana gogewar da suka samu cewa ba ta da ta biyu a tarihin hada-hadar man fetur da iskar gas a Najeriya, sun yi nuni da cewa Najeriya ba za ta kara shiga cikin matsalar man fetur ba, da zarar Matatar dangote ta fara aiki ka’in da na’in.
Kamfanin Matatar dangote ya shirya fara aiki gadan-gadan don haka ya tura rukunin injiniyoyinsa zuwa matatar mai ta Bharat da ke kasar Indiya, wadda aka tabbatar da cewa ta fi kowace matata girma a duniya, musamman kan al’amarin da ya shafi horarwa a aiki.
kasar nan ta zaku ta ga Matatar dangote ta fara aiki, inda za ta rika samar da tataccen man fetur gangan dubu 650 a kullum da zarar ta fara aiki, musamman a daidai wannan lokaci da matatun kasar nan hudu suka durkushe.
Da suke bayyana gogewar da suka samu a horon da aka tura su, injiniyoyin daya bayan daya sun mika wa Hukumar Gudanarwar Matatar a farfajiyarta da ke Lekki a Jihar Legas kwafen horon da suka samu a rubuce da tsarin aiwatar da aiki a aikace da suka yi a kasar Indiya, kuma sun yi sa’a wajen ganin yadda aka fara gina matatar dangote tun daga tushe.
Opeyemi Oyedepo, injiniyan tafiyar da aiki da Igwe John injiniyan sarrafa albarkatun man fetur da iskar gas, sun bayyana wa hukumar gudanarwar yadda suka kasance a rukunin masu warware matsaloli a lokacin horarwar, wani ci gaban da ya kara musu kwarin gwiwa shi ne kasancewar Matatar dangote tana da kayan aiki na zamani kuma za ta iya kawar da matsalar karancin man fetur da ake ta fama da ita a Najeriya.
Da suke bayani kan alfanun horarwar ga Matatar dangote, injinyoyin sun ce kamfani zai samu karin kwararru da karin kwazon aiwatar da ailki, ta yadda za a cimma burin da aka kudurta a kan kari.
Injiniyoyin da suka samu horon sun jero dimbin alfanun ingantuwar aiwatar da ayyukan matatar wajen tabbatar da nagarta da kimar darajar abin da ake samarwa.
A nasa sharhin, kwararren mai bayar da shawara ga Matatar dangote, Injiniya Babajide Soyode ya nuna gamsuwarsa kan cewa an an zabo zakakuran injiniyoyikamar yadda masu bayar da horon suka tabbatar a Indiya.
Ya ce hukumar gudanarwar tana alfahari da su, kamar yadda suka nuna cikakkiyar fahimta kan abin da suka koyo a kasar Indiya.
Dangane da dalilin da ya sanya aka zabi kasar Indiya don horarwar, Injiniya Soyode ya ce Indiya tana da matatar mai mafi girma a duniya, kuma a shirye suke su horar da matasan injiniyoyinmu, sabanin yadda lamarin yake a Turai da sauran Yammacin duniya.
Daraktan da ke kula da ma’aikata, Mohan Kumar, lokacin da yake gabatar da injinyoyin da suka dawo ya ce kamfanin yana kafa kwararran tushe don fara hada-hadar ayyuka tare da injiniyoyin da suka samu horon.
Ya ce matasan injiniyoyin sun samu horo a kamfanin sarrafa albarkatun fetur na Bharat da ke Indiya kan yadda za su gudanar da ayyukan matatar.
Kumar ya yi karin haske cewa injiniyoyin sun samu ilimin dabarun ayyuka a aikace game da matatar.
A cewarsa, injiniyouyin an dauke su ne an horar da su kan yadda ake kafa matata daga tushe. Ya ce injiniyoyin sun shafe wata biyu a aji suna samun horo da kuma wata uku na horon aiki a aikace.
Kumar ya bayyana yadda kwararru kuma gogaggu a sama da shekara 45 a harkar gudanar da matatar mai suka horar da injiniyoyin kan ayyuka, inda ya yi nuni da cewa horon na da muhimmanci saboda jajircewar rukunin kamfanonin dangote wajen bunkasa albarkatun cikin gida, tare da bunkasa dabarun ’yan kasa.
A cewarsa: “Injiniyoyin ana sa ran za su yi amfani da dabarun da suka koyo don hidima ga ’yan Najeriya da zarar matatar ta fara aiki.”