Mun yi asara mai yawa – Mutanen da gobarar tanka ta shafa

Masu shaguna da masu motoci da gidaje da gobarar tankar mai ta yi wa barna a daidai mahadar yankin Yanapaja da ke Jihar Legas sun bayyana yawan asara da hadarin da gobarar ta janyo musu. Wasu daga cikinsu sun bayyana wa Aminiya cewa gobarar ta janyo musu asarar da ta karya jarinsu wasu kuwa cewa […]

Mun yi asara mai yawa – Mutanen da gobarar tanka ta shafa
Mun yi asara mai yawa – Mutanen da gobarar tanka ta shafa

Masu shaguna da masu motoci da gidaje da gobarar tankar mai ta yi wa barna a daidai mahadar yankin Yanapaja da ke Jihar Legas sun bayyana yawan asara da hadarin da gobarar ta janyo musu.

Wasu daga cikinsu sun bayyana wa Aminiya cewa gobarar ta janyo musu asarar da ta karya jarinsu wasu kuwa cewa suka yi ba su da kudin da za su gyara shagunansu.
Wani mai suna Mista Philip Nwako cewa ya yi gobarar ta kone masa hajarsa baki daya. “Ni babu abin da zan ce don gobarar ta kone shagona baki daya. Kuma maganar da nake yi da kai a yanzu ba ni da kudin da zan mayar da kayan da gobarar ta kone, don sun kai kayan Naira miliyan bakwai. Sannan kuma akwai kudaden jama’a a cikin shagon, ban san yadda zan yi da mutanen da na karbo kaya daga wurin su ba. Jiya na karbo kaya masu yawa daga wurin maigidana da zummar zan biya shi cikin makon da muke ciki sai ga wannan bala’i ya auku.” Inji shi.
Shi ma Taiwo Abiodun cewa ya yi gobarar ta saka shi cikin tsaka mai wuya. “Na shiga halin ni-’ya-su. Ban san yadda zan yi ba. Ina gida aka kira ni aka ce mani tanka ta fadi kuma har wutar ta kama shagunanmu. Kafin na iso wurin duk shagunanmu da ke bakin titi sun kone. Ga shi kwananan na gama biyan kudin gidan da na kama haya kuma nan da ’yan watanni zan biya kudin makarantar yara. Na kwashe kudina baki daya na sayo kaya yanzu zancen da nake yi da kai ba ni da ko taro.” Inji shi.
Lateefat Taiwo da ke sayar da kayan yau da kullum a wurin ta bayyana cewa gobarar ta janyo mata asarar kimanin Naira miliyan biyu. “Saboda haka ina kira ga gwamnati ta tallafa mana yadda za mu samu mu gyara shagunanmu mu koma bakin kasuwancinmu. Da wannan kasuwancin muka dogara, da shi muke ciyar da iyalanmu. Ba ma aikin komai sai wannan kasuwancin. Don Allah a zo a taimaka mana.” Kamar yadda ta koka.
Wadanda lamarin ya auku a kan idonsu sun bayyana cewa tankar ta fado ne daga kan gadar yankin Yanapaja yayin da direban yake tuki. Sai dai wasu sun bayyana cewa lamarin ya auku da tsakar daren Litinin, wasu kuwa suka ce lamarin ya auku da sanyin safiyar ranar Talata.
Binciken Aminiya ya gano cewa shaguna fiye da 20 da gidaje 10 da motoci 17 da mutane kimanin 40 sun kone. Tuni hukumar kashe gobara ta jihar ta shawo kan gobarar amma kuma hanyar da lamarin ya auku ta cunkushe da motoci.
Jim kadan da isa wurin da lamarin ya auku, Gwamnan Jihar Legas, Akinwunmi Ambode ya dora alhakin gobarar tankar man ga tukin ganganci da kuma rashin da’a na direbobin tanka. Ya bayyana cewa tuni hukumomin da ke kashe gobara hudu na jihar suna isa wurin kuma tuni suka shawo kan lamarin.
“Wannan ya nuna cewa ya zama dole direbobin tanka su yi wani abu cikin gaggawa don maganin aukuwar wannan lamari a gaba. Ba za mu bari ana samun asarar rayuka da dukiyoyi ba sakamakon tukin ganganci da rashin da’a na direbobin tanka a jiharmu ba.” Inji shi