Mun yi asarar miliyoyin Naira a gobarar kasuwarmu -’Yan kasuwar Daleko

Gobarar da ta tashi a kasuwar mai ta Daleko da ke yankin Mushin a Jihar Legas sakamakon katsewar wutar lantarki ta jawo wa ’yan kasuwar asarar miliyoyin Naira.An kiyasta cewa gobarar ta kone shaguna fiye da 120 tare da hajojin ’yan kasuwar bila adadin, amma babu asarar rai ko jikkata.Wata mai sayar da man kuli […]

Mun yi asarar miliyoyin Naira a gobarar kasuwarmu -’Yan kasuwar Daleko
Mun yi asarar miliyoyin Naira a gobarar kasuwarmu -’Yan kasuwar Daleko

Wani sashe na cin wuta a kasuwar Daleko da ke Jihar LegasGobarar da ta tashi a kasuwar mai ta Daleko da ke yankin Mushin a Jihar Legas sakamakon katsewar wutar lantarki ta jawo wa ’yan kasuwar asarar miliyoyin Naira.
An kiyasta cewa gobarar ta kone shaguna fiye da 120 tare da hajojin ’yan kasuwar bila adadin, amma babu asarar rai ko jikkata.
Wata mai sayar da man kuli mai mai suna Alaja Tasurat Abiodun  ta bayyana cewa ta yi asarar kayan da suka kai na fiye da naira miliyan biyu sakamakon gobarar.
Ta ce: “Da misalin karfe biyu na daren ranar Lahadi, sai wani makwabcina ya kira ni ta wayar salula, ya ce mini kasuwarmu ta kama da wuta. Lokacin da na je wurin sai na tara komai ya kone. Duk abin na tara a rayuwata na sanya shi a jarin shagon, yanzu komai ya kare. Ta ina zan fara?”
Wani dan kasuwa mai suna Ishaku Ajimobi ya bayyana cewa ya yi asara mai tarin yawa.
“Na yi asarar kayayyakina da suka kai na kimanin Naira miliyan biyu. Duk abin da nake sayarwa sun kone kurmus babu abin da ya rage.”
Alhaji Apoola da ke sayar da shinkafa ya ce gobarar ta lashe buhuhunan shinkafarsa 100.
“Gobarar ta cinye buhuhunan shinkafata baki daya. Komai ya kone.” Inji shi.
Ya bukaci Gwamnatin Jihar Legas da masu hannu da shuni su tallafa musu ta hanyar kawo musu dauki.
Janar manaja na Hukumar Taimakon Gaggawa na Jihar Legas Dokta Femi Oke ya ziyarci kasuwar don ganewa idonsa abin da ya faru.
Ya ce Gwamna Babatunde Fashola ya umurci su tantance barnar da gobarar ta yi da wadanda lamarin ya shafa don a taimaka musu.