Mun yi aure rana daya, matanmu sun haihu rana daya – Tagwaye ’yan shekara 72

A Jihar Sakkwato an samu ’yan tagwaye masu shekara 72, wadanda suka yi aure rana daya, kuma matansu suka haihu a rana guda. Tagwaye Hassan da Husaini, suna zaune ne a Unguwar ’Yarkatanga da ke cikin birnin Sakkwato a kan titin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello. Wadannan ’yan tagwaye masu kama daya ana matukar girmama su […]

Mun yi aure rana daya, matanmu sun haihu rana daya – Tagwaye ’yan shekara 72

DCCver0076

A Jihar Sakkwato an samu ’yan tagwaye masu shekara 72, wadanda suka yi aure rana daya, kuma matansu suka haihu a rana guda. Tagwaye Hassan da Husaini, suna zaune ne a Unguwar ’Yarkatanga da ke cikin birnin Sakkwato a kan titin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello. Wadannan ’yan tagwaye masu kama daya ana matukar girmama su a cikin al’umma, saboda kusan kodayaushe a tare suke.
Aminiya ta gano cewa, hatta tufafin da ’yan biyu ke sanyawa iri daya ne, da agogonsu da takalmansu da zobbansu, wadannnan datijan ’yan biyu, wadanda magidanta ne, sun bayyabna cewa suna matukar sha’awar sanya kaya iri daya. Wani abin al’ajabi game da ’yan biyun, shi ne duk suturar da suka sanya sai ta yi musu cif-cif. Kuma suna da sana’a iri daya, wato duk teloli ne.  Abinci ma tare suke ci, domin matasu n agama girki a lokaci daya, kamar yadda suka bayyana.
Abin da ya bambanta ’yan tagwaye kawai shi ne, a cikin ’ya’ya 11 da Hassan ya Haifa ya samu tagwaye, amma shi Hussaini a nasa ’ya’yan tara babu tagwaye.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan