Mun yi bankwana da ECOWAS babu batun dawowa – Nijar, Mali da Burkina Faso
Ƙasashen uku sun jaddada aniyarsu na ficewa daga ƙungiyar ECOWAS.
Ƙasashen Mali, Nijar da Burkina Faso, waɗanda suka ƙulla sabon ƙawance, sun sake tabbatar da matsayarsu na ficewa daga Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS).
Ƙasashen sun bayyana wannan matsaya ne yayin wani taro da ministocin harkokin wajen ƙasashen suka gudanar a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, a ranar Juma’a.
- Majalisar Dattawa ta buƙaci Wike ya dakatar da rusau a Abuja
- Zamana a gidan yari jarabawa ce daga Allah – Farouk Lawan
Taron ya mayar da hankali kan samar da hanyoyin da za su bai wa jama’arsu damar yin zirga-zirga tare da samun damar gudanar da kasuwanci cikin sauƙi a faɗin yankin.
Haka kuma, ministocin sun bayyana aniyarsu na kafa kwamitin ƙwararru da zai nazarci hanyoyin da za su tabbatar da cewa ficewar ƙasashen ba za ta kawo wa jama’arsu matsala ba.
Wannan mataki yana nufin kare buƙatun jama’arsu yayin da suka yanke hulɗa da ECOWAS.
Ficewar ƙasashen uku daga ECOWAS ta samo asali ne daga taƙaddamar da ta kunno kai bayan juyin mulki da aka yi a ƙasashen.
Ƙungiyar ECOWAS, ta sanya wa ƙasashen takunkumi, ciki har da kulle iyakokinsu da hana su zirga-zirga da kasuwanci.
Ƙasashen Mali, Nijar da Burkina Faso sun yi Allah-wadai da matakin, inda suka yi zargin takunkumin ya ƙara ta’azzara wahalar rayuwa ga al’ummarsu.
A watan Agustan 2023, ƙasashen uku sun ƙulla sabon ƙawancen domin ƙarfafa haɗin kai, tsaro, da kuma kare muradunsu a yankin Sahel.
Wannan ƙawance ya maye musu gurbin ECOWAS, tare da mayar da hankali kan tsaron iyakokinsu da kare yankunansu daga barazanar ta’addanci.
A halin yanzu, ECOWAS ta amince ta tsawaita wa’adin tattaunawa don shawo kan ƙasashen domin su janye ƙudirinsu, amma sun bayyana ƙarara cewa sun gama ficewa daga ECOWAS.
Sun ce babu batun dawowa kuma za su ci gaba da haɗa kansu don ganin yankin Sahel ya kasance cikin zaman lafiya da samun ci gaba ba tare da dogaro da ECOWAS ba.