Mun yi farin ciki da karya kwarin Enyimba – Henlong

Kyaftin din kungiyar kwallaon kafa ta Giwa da ke Jos a Jihar Filato Charles Henlong ya ce sun yi farin ciki da suka karya wa kulob din Enyimba na garin Aba a Jihar Abiya kwarin yin wasa 10 ba tare da rashin nasara ba.Kyaftin Henlong ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da […]

Mun yi farin ciki da karya kwarin Enyimba – Henlong
Mun yi farin ciki da karya kwarin Enyimba – Henlong

Kyaftin din kungiyar kwallaon kafa ta Giwa da ke Jos a Jihar Filato Charles Henlong ya ce sun yi farin ciki da suka karya wa kulob din Enyimba na garin Aba a Jihar Abiya kwarin yin wasa 10 ba tare da rashin nasara ba.
Kyaftin Henlong ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya bayan an tashi wasa tsakanin kulob dinsu da Enyimba a filin wasa na Rwang Pam da ke Jos a ranar Lahadi.
Henlong wanda shi ne ya jefa wa kulob dinsa kwallo a raga yayin wasan ya yaba wa ’yan wasansa bisa jajircewar da suka yi wajen ganin ba a ci su a wasanni biyar na karshe da suka buga ba, inda suka samu nasara a wasa uku, suka yi kunnen doki biyu.
“Wasa ne tsakanin giwaye biyu, inda giwar Aba ta yi wasa 10 ba tare da an yi nasara a kanta ba, muna sane da cewa ba su taba samun nasara a wasa uku da muka yi da su ba, tunda muka fara buga gasar Premier a bara, hakan ya ba mu karfin gwiwar ganin ba su samu nasara a kanmu ba. Daga nan muka sha alwashin wannan ne lokacin mafi dacewa da ya kamata Enyimba ta dandana rashin nasara a hannunmu, sannan kocinmu ya umarce mu da mu buga wasa zafi-zafi, kada mu bari su sarara a kan kwallon, inda a karshe hakarmu ta cimma ruwa,” inji shi.
Ya ce: “Zan kuma yi amfani da wannan dama wajen yaba wa ’yan kulob dina bisa kwazon da suka nuna a wasanni biyar da muka buga ba tare da an yi nasara a kanmu ba. Hakan ba karamin abin alfahari ba ne a gasar Premier ta Najeriya mai cike da kalubale da dama, ina taya mu murna.”
Charles ya samu nasarar jefa kwallo ne a minti na 74 bayan da kungiyarsa ta kai wani mummunan hari a gidan Enyimba, inda dan wasan baya mai suna Anyanwu ya tare kwallon da hannu aka buga finareti.
Daga karshe ya bukaci ’yan kungiyarsa su tashi tsaye tare da zage damtse don ganin sun cimma burinsu na buga wasan Zakarun Afirka a badi.