Mun yi kudirin tara Naira miliyan 500 a Disamba – Masu garkuwa da mutane
Wadansu da ake zargi da fashi da makami da yin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa sun ce sun shirya tsaf da nufin tara Naira miliyan 500 a watan Disamban nan ta hanyar yin garkuwa da manyan ’yan kasuwa a Abuja da Kaduna. Rundunar ’yan sanda ta musamman (IRT) da ke yaki da miyagun […]
Wadansu da ake zargi da fashi da makami da yin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa sun ce sun shirya tsaf da nufin tara Naira miliyan 500 a watan Disamban nan ta hanyar yin garkuwa da manyan ’yan kasuwa a Abuja da Kaduna.
Rundunar ’yan sanda ta musamman (IRT) da ke yaki da miyagun ayyuka ta hanyar bin diddigi da amfani da kimiyyar zamani ce ta katse hanzarin masu garkuwa da mutanen, bayan da Babban Sufeton ’Yan sandan Najeriya, Alhaji Ibrahim K. Idris ya ba da umarnin a kamo wadanda ake zargin, sakamakon takardar koke da iyalin wani mutum da aka yi garkuwa da shi suka shigar, lamarin da ya yi sanadiyyar kame masu kitsa garkuwar tare da yanke burinsu na tara Naira miliyan 500.
Daya daga cikin wanda ake zargin mai suna Sani Muhammad, ya shaida wa manema labarai lokacin da ake gabatar da su, cewa shi dan asalin Jihar Zamfara ne wanda yake yin sana’ar kiwon shanu. Ya ce a shekarar 2007 ya je Abuja inda ya samu maigida Alhaji Ulere wanda ya yi wa aikin kiwon shanu, amma bayan wani lokaci suka raba gari bisa zarginsa satar saniya, inda ya koma Enugu wajen abokinsa wanda shi ma makiyayi ne.
Ya ce ko da ya riski abokin nasa a Enugu sai ya tarar da shi a cikin wasu gugun ’yan fashi da makami inda shi ma ya shiga suka ci gaba da aikin tare. Ya ce sun yi ta tare babbar hanyar Enugu zuwa Fatakwal suna fashi sannan su yi garkuwa da wadanda suke da alamum hannu da shuni, inda suke tsare su har sai sun biya kudin fansa.
Ya ce asirinsu ya tonu ne bayan da ya bai wa abokan fashinSA labarin tsohon uban gidansa wanda ya shaida mUsu mutum ne attajiri da ke da tarin dukiya, kuma yana zaune ne a Abuja. Don haka suka nufi Abuja da zimmar yin garkuwa da tsohon maigidan nasa Alhaji Ulere, inda da isarsu ya kira wayarsa ko da ya zo suka yi garkuwa da shi, sai dai asirinsu ya tonu ne bayan da iyalin Alhaji Ulere suka sanar da jami’an ’yan sandan kan batun.
Sani Muhammad ya shaida cewa da a sirinsu bai tonu ba da sai sun tara zunzurutun kudi Naira Miliyan 500 a watan Disamban nan ta hanyar yin garkuwa da attajirai a Abuja da Kaduna.
Wadanda rundunar ’yan sandan ta kame sun hada da Babangida Garba da Dogo Ibrahim sai Ibrahim Haruna. A cewar Ibrahim Haruna shi ke karbar kaso mafi yawa a kudin da suka samu domin shi ke da bindigar AK47 wace ya sayo ta a Jos a kan Naira dubu 450, ya ce ya yi nadamar shiga aikin garkuwar da ya yi sanadiyyar kama su, “Muhammad Sani ne ya gayyato ni na zo Abuja mu yi garkuwa da Alhaji Ulere,” inji shi.
Babangida Garba, daya daga cikin wadanda ake zargin, ya ce sun shiga Abuja ne suka yi garkuwa da Alhaji Ulere, “Mun bukaci a ba mu Naira miliyan 10 kudin fansa, ba mu da masaniyar cewa iyalansa sun fada wa ’yan sanda, koda Dogo ya je ya karbo kudin sai aka kama shi, da muka samu labarin haka sai muka sake shi muka gudu,” inji shi.
Kakakin ’Yan sanda na Kasa Mashood Jimoh ya shaida wa manema labarai cewa wadanda ake zargin Fulani masu dauke da makamai da suka kware a shirya fashi da makami da garkuwa da mutane domin karbar kubin fansa.
Ya ce Rundunar IRT kama su ne a karkashin jagorancin Mataimakin Kwaminshinan ’Yan sanda Abba Kyari, kuma an same su da bindiga kirar AK47 da wasu bindigogin gida guda uku.