Mun yi kusan ganin bayan Boko Haram – Sojoji

Mukaddashin  Daraktan Labarai na Hedkwatar Tsaro Kanar Rabe Abubakar ya ce an yi kusan kawo karshen hare-haren Boko Haram a kasar nan.Kanar Rabe Abubakar, ya bayyana haka ne a ranar Litinin lokacin da wasu manema labarai sula ziyarce shi a ofishinsa da ke Hedkwatar Tsaro a Abuja.Kakakin hedkwatar tsaron, kamar yadda wata sanarwa dauke da […]

Mun yi kusan ganin bayan Boko Haram – Sojoji
Mun yi kusan ganin bayan Boko Haram – Sojoji

Mukaddashin  Daraktan Labarai na Hedkwatar Tsaro Kanar Rabe Abubakar ya ce an yi kusan kawo karshen hare-haren Boko Haram a kasar nan.
Kanar Rabe Abubakar, ya bayyana haka ne a ranar Litinin lokacin da wasu manema labarai sula ziyarce shi a ofishinsa da ke Hedkwatar Tsaro a Abuja.
Kakakin hedkwatar tsaron, kamar yadda wata sanarwa dauke da sanya hannu Laftana Kwamanda Way Olabisi ta ce, ya bayar da misali da sabon yunkurin da shugabannin soji ke yi da kuma tashi tsaye da sojojin da ke bakin daga suka yin a ceto yankin da lamarin ya yi kamari tare da kawo karshen hare-haren.
Ya yaba hadin kan da ake samu a tsakanin sojin kasa da na sama a kokarin da ake yin a tuttuge Boko Haram daga inda take da karfi ciki har da sansanoni da dama da suke dajin Sambisa.
Kanar Abubakar ya ce rashin kishin kasa ne wani dan kasa ya dauki makami bisa kowane dalili ya kama kashe mutanensa da kasarsa, inda ya yi kira ga ’yan Boko Haram kan”su sake tunani su ajiye makamansu tare da watsi da bakuwar akidarsu domin tabbatar da jin dadin rayuwar dan Adam.”
Sai ya jinjina wa sojojin da suke fagen-daga kan “Tsayuwar Dakar da suke yi wajen kawar da duk wani nau’i na ayyukan ta’addanci,” inda ya jingina nasarorin da suke samu a yanzu kan karfin gwiwa da samar musu da makamai wajen fuskantar abokan gaba a fagen yaki.
Game da hare-haren kunar bakin wake, Kanar Abubakar ya tabbatar wa jama’a cewa Hedkwatar Tsaro tana sake tsara dabaru wajen magance su.
Ya kawo misali da yadda wani dan kunar bakin wake ya yi yunkurin tayar da bam a tashar mota ta Yankari da ke garin Bauchi amma aka kama shi kafin ya ida mugun nufinsa, sai ya yi kira ga jama’a su rika kasancewa a fadake lokacin da suke cikin taron jama’a, ciki har da kasuwanni da wuraren ibada.
Kuma ya bukaci jama’a su hada hannu da sojoji da sauran jami’an tsaro wajen bayar da bayanan da za su taimaka wajen magance ayyukan ’yan ta’adda a kan lokaci.