Mun yi murna da cire jami’an tsaro

Assalamu alaikum Aminiya, ku bani dama nayi tsokaci dangane da wasu sabbin matakai da shugaba Buhari ya dauka a baya bayannan, inda ya bada sanarwar gusar da daukacin tashoshin bincike “Check-point” dake wuraren dake sassan kasar nan da zaman lafiya ke zama da gindinsa, muma muna addu’ar Allah Ya nuna mana lokacin da za’a gusar […]

Mun yi murna da cire jami’an tsaro
Mun yi murna da cire jami’an tsaro

Assalamu alaikum Aminiya, ku bani dama nayi tsokaci dangane da wasu sabbin matakai da shugaba Buhari ya dauka a baya bayannan, inda ya bada sanarwar gusar da daukacin tashoshin bincike “Check-point” dake wuraren dake sassan kasar nan da zaman lafiya ke zama da gindinsa, muma muna addu’ar Allah Ya nuna mana lokacin da za’a gusar da wadanda ke garkame a garuruwanmu da ‘yan ta’adda ke kai farmaki, kana ina kara fatan alheri ga shugaba buhari dangane da gargadin da yayi wa gwamnoni kan almundahana da taka dokokin kasa, wannan mataki yayi domin ko ba komai, mahandama zasu shiga taitayinsu tare da yin taka tsan tsan. Daga karshe nake kira ga masu hannu da shuni da su taimakawa dubban ‘yan gudun hijra dake warwatse a kasar nan albarkacin wannan wata mai alfarma. Kana ‘yan kasuwa suji tsoron Allah su rage farashin kaya saboda cin gajiyar Ramadana. Domin abinda ba su samu samu a watanni goma sha daya ba, to da wuya su samu cikin wata daya, Allah Ya sa mu dace. Aameen. Daga Sakatare Usman Bin-Affan Damaturu, Jihar Yobe. 08038001563