Mun yi rashi

Allah Ya yi wa Malam Umaru B and B, wanda shi ne shugaban masu raba jaridu, da ke kula da jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara rasuwa.Marigayin ya rasu ne sakamakon fama da ciwon suga da hawan jini da ya yi. Malam Umaru B and B, ya rasu ya bar matar aure daya da ’ya’ya […]

Mun yi rashi
Mun yi rashi

Allah Ya yi wa Malam Umaru B and B, wanda shi ne shugaban masu raba jaridu, da ke kula da jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara rasuwa.
Marigayin ya rasu ne sakamakon fama da ciwon suga da hawan jini da ya yi. Malam Umaru B and B, ya rasu ya bar matar aure daya da ’ya’ya takwas, kuma an ce ya shafe shekara 30 yana harkar raba jaridu.
Marigayin wanda ya rasu a ranar Talatar da ta gabata da misalin karfe 5:30 na safe, tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista