Mun yi rashi
Allah Ya yi wa Limamin Unguwar Shagari da ke garin Bauchi Malam Yusuf Musa Yusuf wanda aka fi sani da Malam Babangida rasuwa. Marigayin ya rasu ne sakamakon hadarin mota da ya rutsa da shi a hanyar Jos zuwa Bauchi a ranar Litinin. Mai shekara 51 Malam Babangida wanda aka haifa a garin Gembau da […]
Marigayi Malam Babangida
Allah Ya yi wa Limamin Unguwar Shagari da ke garin Bauchi Malam Yusuf Musa Yusuf wanda aka fi sani da Malam Babangida rasuwa.
Marigayin ya rasu ne sakamakon hadarin mota da ya rutsa da shi a hanyar Jos zuwa Bauchi a ranar Litinin. Mai shekara 51 Malam Babangida wanda aka haifa a garin Gembau da ke Gundumar Garga ya rasu ya bar matan aure biyu da ’ya’ya 12 da kuma ’yan uwa da dama.
An yi masa Sallar Jana’iza a ranar Talata a kofar gidan Babban Limamin Bauchi Malam Bala Baban Inna.
Allah Yajikansa da rahama