Mun yi sa’a da Najeriya ta abka cikin babban bala’i – Jonathan da Bakare
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan da Mataimakin Buhari a zaben 2011, Fasto Tunde Bakare sun ce saura kiris kasar nan ta fada cikin babban bala’i in da wadanda suka dana bama-bamai sun samu nasarar halaka tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari da fitaccen malamin addinin Musulunci nan Sheikh dahiru Usman Bauchi.Shugaba kasar ya ce da […]
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan da Mataimakin Buhari a zaben 2011, Fasto Tunde Bakare sun ce saura kiris kasar nan ta fada cikin babban bala’i in da wadanda suka dana bama-bamai sun samu nasarar halaka tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari da fitaccen malamin addinin Musulunci nan Sheikh dahiru Usman Bauchi.
Shugaba kasar ya ce da masu harin bAm sun samu nAsarar kashe Janar Buhari a harin da suka kai amsa ranar Larabar makon jiya a Kaduna da kasar ta shiga cikin mummunan rikici. Shugaba Jonathan ya yi wannan bayanin ne a lokacin da ya tarbi tawagar mazaunan Birnin Tarayya, Abuja, da suka kai gaisuwar Sallah, inda ya ce Allah Ya ceci kasar nan daga afkawa cikin rikici, ta hanyar kare rayukan tsohon Shugaban kasar da malamin Musuluncin.
“Hare-haren baya-bayan nan da aka kai Kaduna, musamman wadanda aka nufi Sheikh dahiru Bauchi, wanda babban mai wa’azin Musulunci ne da ke da miliyoyin mabiya da Janar Buhari, wanda tsohon Shugaban kasar nan ne, kuma jigo a siyasa da ke da dimbin magoya baya. Kuma a rana guda mutane suka yi kokarin halaka su, wani shiri ne na wargaza kasar nan,” inji shi.
A cewarsa: “Wadanda suka shirya harin ta bayyana karara shaidanu ne, saboda da sun kashe wadannan mutum biyu, ba za ta yiwu mu taru a inda muke a yau ba. Ba za ta yiwu mu yi taron murnar wanan ranar ba. Mun gode Allah da Ya tserar da rayukansu, Ya kawar mana da mummunaar masifa da ta kusa auka wa kasarmu.”
Jonathan ya ce wadannan shugabanni biyu su aka nufa da wannan hari. Kuma ya soki lamirin hare-haren da aka kai a Kaduna da Kano, ina ya ce, “Mun yi tir da wadannan ayyukan ta’addanci da aka kaddamar a kan mutanenmu. Kuma muna mika ta’aziyya da jaje ga wadanda suka rasu da wadanda suka samu raunuka.”
Shugaban ya roki malaman addini suka rika gabatar da wa’azin zaman lafiya da hadin kai.
“Ina rokon ’yan uwana, musamman malaman addini cewa a lokacin da suke isar da sakonni ga mabiyansu, su rika yin wa’azin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai, don rashin zaman lafiya da hadin kai ba za su ba mu damar gina wannan kasar ba,” inji shi.
Ya ce: “A lokacin rikici, mutane na yin kaura daga irin wadannan yankuna ta yadda ba za mu iya bunkasa al’ummomin kananan hukumominmu da jihohi da ma kasarmu a yanayi na tashin hankali ba.”
Jonathan ya roki ’yan Najeriya da su ba gwamantinsa hadin kai don kawo “karshen Boko Haram da sauran kungiyoyin ta’addanci.”
Sannan ya bayyana kafa gidauniyar neman tallafi don taimakon matan da mazajensu suka mutu da marayu da wadanda aka lalata harkokin kasuwancinsu da wuraren ibada da suka hada da masallatai da coci-coci, “duk za mu gina su.”
Daga bisani Mataimakin Shugaban kasa Namadi Sambo, wanda ya jagoranci tawagar, ya roki Allah Ya kawo karshen ayyukan ta’addanci a kasar nan.
Tawagar ta kunshi Ministan Birnin Tarayya, Bala Mohammad da tsohon Babban Jojin Najeriya, Salihu Modibbo Alfa Belgore da tsofaffin shugabannin Jam’iyyar PDP na kasa, Bello Halliru Mohammed da Ahmadu Ali da shugaban Kwamitin Majalisar Dattijai kan Birnin Tarayya, Smart Adeyemi.
Shi kuma Fasto Tunde Bakare, Shugaban Majami’ar Letter Rain Assembly, ya bayyana cewa ’yan Najeriya su yi godiya ga Ubangijin ganin cewa yunkurin daukar ran Janar Muhammadu Buhari bai samu nasara ba, ala’amarin da ya ce da ya jefa kasar nan cikin mummunan rikicin da zai haifar da dimbin asarar rayuka.
Tunde Bakare, wanda ya kasance, Maitaimakin Buhari a takarar Shugaban kasa a karkashin rusasshiyar Jam’iyyar CPC a zaben 2011, ya ce Buhari na da miliyoyin magoya baya a Arewa, wadanda za su iya daukar doka a hannunsu.Ya ce wannan rikici na iya bazuwa zuwa Kudu, inda za a yi ta daukar fansa.
Bakare ya bayyana haka ne a wani wa’azi da ya gabatar a cocinsa da Legas ranar Lahadin da ta gabata.
Ya ce sakamakon ayyukan ’yan ta’adda an kashe akalla sama da mutum dubu shida a tsakanin shekarar 2010 zuwa watan Yunin bana, sannan ya ce a bana kadai an kashe sama da mutum 2,500.
Ya gargadi masu tunanin cewa ayyukan ta’addanci al’amura ne da suka shafi Arewa kadai, ya ce bayan tsare wasu ’yan Arewa 486 da ake zargi da ta’addanci a Jihar Abiya, ’yan Boko Haram sun dauki alhakin kai hari a Jihar Legas, a daidai lokacin da gwamnati ke kokarin nuna cewa “fashewar wani abu ne kawai.”
Bakare ya ce abin da ya sanya ayyukan ta’addanci ke kara bunkasa a Najeriya shi ne, gazawar da aka nuna wajen tattara bayanan sirri, inda aka mayar da hankali kacokan wajen bibiyar halin ’yan adawa, maimakon miyagun masu aikata laifuffuka, wadanda su ne makiyan wannan kasa. Sauran dalilan inji shi sun hada da rundunar soja mara katabus da makircin cikin gida da na waje da kuma masu neman cin bulus.
Ya ce harin da aka kai wa Buhari ya tabbatar da cewa Buhari ba ya tausasa wa ’yan Boko Haram. Kuma ya ce sojoji kadai ba za su iya shawo kan ta’addanci ba, inda ya yi nuni da cewa sojoji na tunkarar ’yan Boko Haram da “makamai marasa inganci.”
Ya soki lamirin Shugaba Jonathan kan neman bashin Dala biliyan daya da zai yaki ta’addanci, inda ya ce, “Lokaci na karshe da aka samar wa sojoji kayan aiki shi ne a shekarun 1980, alhali akwai kason da ake warewa a kowane kasafin kudin shekara.”
Ya yi gargadin cewa daina gwama hakiknain Musuluncin da aka sani a al’adance da akidar masu tsattsauran ra’ayin Musulunci, inda ya ce tsattsauran ra’ayin Musulunci da tsarin karba-karba da aka yi wa murdiyya da rashin adalci, suka haifar da ta’addanci.
“Matukar muna son cin nasarar wannan yaki, dole ne mu dauki tafarkin da ya dace. Akwai bambanci tsakanin hakikanin Musuluncin da aka sani a al’adance da tsattsauran ra’ayin Musulunci da muke gani a yau. Gwama su wuri guda ba karamin kuskure ba ne. Babu abin da zai haifar sai kuskure, wanda ke kai wa ga ta’addajnci. Ina fatan wannan zai zama fadakarwa ga gwamnatinmu, dole mu mike tsaye, ta yadda za mu hada karfi wajen shawo kan kisan gillar da ake yi na’addanci,” inji shi.