Mun yi tanaji domin saukaka ambaliyar ruwa – Hukumar NEMA
Aminiya ta samu damar zantawa da shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) Alhaji Sani Sid,i domin jin irin tanajin da hukumarsa ta yi game da hasashen da ake yi cewa a bana za a fuskancin matsalar ambaliyar ruwa, musamman da yake kasar Kamaru tana shirin sako ruwa daga kogin Lobdu, inda shugaban […]

Aminiya ta samu damar zantawa da shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) Alhaji Sani Sid,i domin jin irin tanajin da hukumarsa ta yi game da hasashen da ake yi cewa a bana za a fuskancin matsalar ambaliyar ruwa, musamman da yake kasar Kamaru tana shirin sako ruwa daga kogin Lobdu, inda shugaban ya yi bayani kamar haka:
Aminiya: Kusan kowace shekara sai an fuskanci matsalar ambaliyar ruwa, wane kokari hukumarka take yi don ganin a bana abin ya zo wa jama’a da sauki?
Alhaji Muhammad Sani Sidi: Tun bayan ambaliyar ruwa da kasar nan ta fuskanta a shekarar 2012, wanda ya shafi kusan rabin jihohin kasar nan, inda hukumarmu ta fuskanci aikin samar da agaji mai girma, gwamnatin tarayya ta umarci a tayar da jama’a daga yankunan da ke iya fadawa matsalar ruwa a sakamakon kusancinsu da rafuka, wanda a turance ake kira “Flood prone areas’’, kowace shekara muna jaddada kira ga gwamnatocin jihohin irin wadannan yan kuna da su tabbata al’ummarsu ba su koma yankunan ba. Muna sane da cewa jama’an ba sa son barin wuraren saboda alherin da su ke samu a sana’o’insu na kamun kifi ko noma, musamman na rani, sai dai a kullum muna nuna musu cewa rayukansu ya fi komi da suke tunanin za su samu. Ina fata gwamnatocin irin wadannan jihohin za su ci gaba da sauke nauyinsu na tabbatar da cewa al’ummarsu ba su koma ba.
Aminiya: Al’ummar da ke iyaka da yankunan da rafukan kasashen Kamaru da Nijar suka hadu da nasu suna cike da fargabar sako musu ruwa daga madatsun ruwan wadannan kasashen, ko akwai wata fahimtar juna a tsakaninku da hukumomin kasashen?
Alhaji Muhammad Sani Sidi: kwarai kuwa, bayan wannan ambaliyar ruwa da na yi maka bayani ta shekarar 2012, gwamnatin tarayya a lokacin ta aika da tawaga zuwa kasar Kamaru tare da jami’an ma’aikatar ruwa da hukumarmu, inda muka sanar da gwamnatin kasar Kamaru irin barnar da lamarin ya yi mana a sakamakon rashin sanar da mu za a bude madatsar ruwan, ko kuma sun sanar amma a kurarren lokaci. To tun daga wancan lokacin suka dauki alkawarin za su rika sanar da mu idan sun tashi bude madatsar a duk shekara, kuma a irin hakan kamar mako guda ke nan yanzu sun sanar da mu aniyarsu ta bude ruwan, nan ba da dadewa ba, bayan mun samu sanarwar mun hanzarta rubuta takarda ga gwamnatocin jihohi da lamarin zai shafa tare da nuna masu bukatar hanzarta tayar da jama’a da ke da kusanci da rafuka don ganin barnarsa bai yi muni ba.
Aminiya: Masana sun bayar da shawara a lokacin na bukatar gina madatsar ruwa a bangaren Najeriya da ke iyaka da na Kamaru, Ina aka kwana?
Alhaji Muhammad Sani Sidi: Lallai haka ne akwai bukatar yin hakan, sai dai ina ganin ma’aikatar ruwa ya kamata ta yi maka wannan bayanin, na tabbata idan ka je can za ka samu cikakken bayani a wajensu wanda zai amsa tambayarka.
Aminiya: bayan yawan hare-haren ta’addanci da kasar Kamaru ta fuskanta a dan tsakanin nan, a kwanan nan sun taso keyar ’yan gudun hijiran Najeriya masu yawa, wane hali suke ciki a yanzu bayan dawo da su?
Alhaji Muhammad Sani Sidi: Haka ne kasar Kamaru ta dawo da jama’armu kamar dubu goma sha biyu ta iyakar kasar nan da ke yankin Mubi na jihar Adamawa. Hukumarmu da sauran hukumomi kamar na tsaro da na shige da fice mun je wajen mun karbe su, kuma yanzu haka kowane bangare na hukomomin nan na aikinsa, wanda ya hada da ciyar da su da tantancesu da kuma samar musu da matsuguni, haka nan ana gudanar da aikin ne tare da taimakon jami’an gwanatin jihar Borno, don tabbatar da cewa ’yan kasa ne gaba dayansu kuma babu bata-gari a cikinsu. Yanzu haka mun tantance kamar mutum dubu takwas kuma an wuce da su zuwa matsugunanmu na ’yan gudun hijira da ke Yola inda za a ci gaba da kulawa da su kafin a kai su yankunansu na asali a nan gaba.