Mun yi zaman amana da marigayi Sarkin Keffi Chindo Yamusa – Sarkin Koro
Sarkin Koro a Jihar Nasarawa Mista Christopher Jatau ya bayyana wa Aminiya cewa sun zaman amana da girmamawa da marigayi Sarkin Keffi Alhaji Muhammadu Chindo Yamusa II.Mista Christopher Jatau Sarkin Kube (Koro) ya ce marigayi Sarki Chindo Yamusa ya taba kasancewa Baturen Ilimi gare shi lokacin da suke koyarwa a firamare kimanin shekara 45 da […]
Sarkin Koro a Jihar Nasarawa Mista Christopher Jatau ya bayyana wa Aminiya cewa sun zaman amana da girmamawa da marigayi Sarkin Keffi Alhaji Muhammadu Chindo Yamusa II.
Mista Christopher Jatau Sarkin Kube (Koro) ya ce marigayi Sarki Chindo Yamusa ya taba kasancewa Baturen Ilimi gare shi lokacin da suke koyarwa a firamare kimanin shekara 45 da suka wuce.
“Lokacin da muke koyarwa a makaranta marigayi Chindo Yamusa mutumin kirki ne kwarai da gaske kuma haziki ne, hakika tun wancan lokacin Sarki Chindo ba ya son munafunci ko rashin gaskiya. Wannan halin nasa ne darajarsa ya daukaka fiye da sauran abokan aikinsa. Ba zan manta ba akwai lokacin da muka taba samun dan sabani da shi wanda da wannan dalilin ne ya sa aka yi masa sauyin aiki zuwa Makurdi daga bisani na gane cewa ni ne da laifi kuma nan take na amsa laifina ba tare da bata lokaci ba ya yafe min, ka ga da irin wannan hali aka san dattijon kirki,” inji Sarkin.
Sai ya ce shugabanci wani abu ne da ke bukatar mutum mai hakuri da iya zama da jama’a kuma a tunanina shugabanci irin na sarauta ya fi dacewa da malamin makaranta, domin sarauta shugabancin ne na har abada, “Malamin makaranta shi ya fi kowa mu’amala da jama’a, kuma a wajen malamin makaranta ake samun tarbiyya, saboda haka zan iya cewa tun a makaranta kowane malami mai sarauta ne ga dalibansa kuma malanta abu ne da har abada ba a mance shi saboda babu malamin da ya san adadin yaran da ya taimaka wajen tarbiyyarsu,” inji shi.
Ya ce wata rana suna hira da marigayi Sarkin Keffi sai ya ce masa halinsa ya dace da sarauta, kuma Allah Ya ba shi sarautar Keffi, ya ce amin. Ya ce “Kai ma Allah Ya ba ka sarautar Koro sai na ce, amin. Allah da ikonSa dukanmu mun cika burinmu kuma mun gode da shaidar da al’umma suke yi mana,” inji Sarkin Koro.
Ya ce, sabon Sarkin Keffi Dokta Shehu Yamusa ya gaji kyawawan dabi’un mahaifinsa na hakuri da rikon amana da son gaskiya da sauransu, inda ya bukaci al’ummar masarautar sub a shi hadin kai don kai yankin gaba.