‘Muna aiki da shawarar Sardaunan Sakkwato ne’

Mai ba Gwamnan Jihar Ondo shawara kan dangantaka tsakanin gwamnati da al’ummar Hausawa mazauna jihar, Alhaji Umaru Abdullahi, ya bayyana cewa sun fara aiki da shawarar marigayi Sardaunan Sakkwato, Sa Ahmadu Bello dangane da yin irin siyasar mutanen da suke tare da su. “Aiki da wannan shawara ya sa mun fara kusantar gwamnati, har da […]

‘Muna aiki da shawarar Sardaunan Sakkwato ne’

Alhaji Umar Abdullahi ke nan (a tsakiya) tare da wasu dattijan Hausawa a ofishinsaMai ba Gwamnan Jihar Ondo shawara kan dangantaka tsakanin gwamnati da al’ummar Hausawa mazauna jihar, Alhaji Umaru Abdullahi, ya bayyana cewa sun fara aiki da shawarar marigayi Sardaunan Sakkwato, Sa Ahmadu Bello dangane da yin irin siyasar mutanen da suke tare da su.
“Aiki da wannan shawara ya sa mun fara kusantar gwamnati, har da cin moriyar tallafin rancen Naira miliyan 30 da Gwamna Olusegun Mimiko ya bayar ga  al’ummar Hausawa domin bunkasa harkokin kasuwancinsu.” Inji shi.
Alhaji Umaru, wanda kuma shi ne shugaban al’ummar ’yan Arewa da ke zaune a jihar ta Ondo ya ce samun tallafin a watan Disamba na bara, ya biyo bayan, “Hada kawunanmu da bayar da gudunmawarmu ga shirye-shiryen gwamnati, musamman ta fuskar samar da zama lafiya da samar da bunkasar tattalin arzikin jihar da kasa baki daya. Wannan ya baiwa Gwamna Olusegun Mimiko sha’awar janyo mu a jika.”
Alhaji Umaru ya bayyana haka ne a hirarsu da wakilinmu a ofishinsa da ke unguwar Sabo a garin Ondo, inda ya kara da cewa, “Bayan mun karbi tallafin rancen, mun kafa kwamitin da ya kwatanta adalci gwargwado wajen rabonsa ga ’yan kasuwarmu da ke ko’ina cikin kananan hukumomi 18 na jihar. Ba mu nuna bambancin addini ko kabila da siyasa ba. Mun yi amfani da cancanta ne ta fannin lura da irin harkar kasuwancin kowane daga cikin wadanda suka samu tallafin. Mun yi yarjejeniyar biyan kudin a cikin shekara daya, kuma gwamna ya tabbatar mana cewa da zarar mun cika alkawari, zai bayar da umarnin a rubanya mana sabon tallafin.”
 Ya ce dayake ba kyauta aka bayar da kudin ba, “Sai muka bayar da su inda za su iya dawowa kudin, kuma sai da kowane daga cikinsu ya cika takardar fom da hotonsa da wani sanannen mai tsaya masa kafin a ba shi kudin, musamman, da yake wannan shi ne irinsa na farko da muka fara samu daga gwamnatin jihar ta Ondo. Mun dauki matakan kauce wa kasawa, kuma tunda yake muna yin wannan fafutuka ne tsakani da Allah domin amfanin jama’armu, muna sa ran kowane bangare zai amfana, domin akwai tanadin nan gaba”.
Dangane da koyi kuwa, sai Umaru Abdullahi ya ce, “kakanni da iyayenmu da suke zaune a wannan sashe, sun sha yi mana bayanin a duk lokacin da Sardaunan Sakkwato, Sa Ahmadu Bello, ya gana da su a ziyarce-ziyarcensa, yana fada musu su goyi bayan jam’iyyar da take mulki a yankin da suke zaune. Yin amfani da wannan shawara ta sa muka ba da cikakken hadin kai da goyon ga Gwamna, wanda tun farko, a lokacin yakin neman zabe, ya nemi hadin kanmu. Bayan ya yi nasara ne muka kai masa ziyarar taya murna, ya yi farin ciki, kuma a nan take ya tabbatar mini da wannan mukami, ya bayar da umarnin ba mu tallafin rance Naira miliyan 30 domin bunkasa harkokin kasuwancinmu.”
Game da rashin jituwa a tsakanin shugabannin Hausawa a sauran jihohi 5 ya yammacin kasa, wacce ta hana su cin irin wannan moriya daga gwamnatocin jihohinsu, sai mai ba Gwamna shawarar ya ce, “A gaskiya dole ne a rika samun rashin fahimtar juna a tsakanin jama’a, amma, idan dai tsakani da Allah ake gudanar da al’amari, to, kuwa ana iya yin maganin komai a taimaka wa juna domin samun ci gaba. Mu ma a nan jihar ta Ondo, mun samu irin wannan sabani, amma bai yi zafin da zai iya hana mu samun wannan matsayi da tallafin ba, domin mun dogara da Allah ne wajen wannan fafutuka da muke yi domin ci gaban mutanenmu. Muna fatan ’ya’ya da jikokinmu a nan gaba za su yi aiki da wannan fafutuka domin ita kadai ce mafita ga mutanenmu da aka bar su a baya. Ba kamar sauran ’yan uwanmu kabilun Yarbawa da Ibo da suke zaune a jihohin Arewa kuma suka dade da fara cin moriyar mahukunta har da manyan mukamai da ake nada su.”
Alhaji Umaru Abdullahi, wanda ya samu kyautukan girmamawa daga wasu fitattun kamfanoni da gidajen jaridu a Jihar Ondo, a dalilin fafutukar lalubo hanyar zama lafiya a tsakanin al’ummarsa da sauran jama’a da ya yi fice a kai, yakan gana da dattijai dadaddun zama da aka kafa unguwar Hausawa a garin na Ondo, “Suna taimaka mana da muhimman shawarwari da sanya mu a mikakkiyar hanya domin ci gaban jama’armu.” Inji shi.