Muna aiki tuƙuru don gyara wutar Arewa — TCN

Lalacewar layin ya yi sanadin rasa wutar lantarki a faɗin Arewacin Najeriya.

Muna aiki tuƙuru don gyara wutar Arewa — TCN

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN), ya ce yana aiki tare da Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro domin gyara wutar lantarkin Arewacin Najeriya.

Lalacewar layin ya yi sanadin rasa wutar lantarki a jihohin Kaduna, Kano, da sauran wasu jihohin Arewacin Najeriya.

Wannan na cikin wata sanarwa da Babban Manajan Hulɗa da Jama’a na TCN, Ndidi Mbah, ya ce suna aiki tuƙuru don gyara wutar lantarki cikin gaggawa.

“Muna jajircewa wajen magance wannan ƙalubale domin mun san muhimmancin wutar lantarki ga rayuwar jama’a da matsalolin da wannan rashin wuta ke haifarwa.

“Mun yi alƙawarin yin duk mai yiwuwa don magance matsalar da dawo da wutar zuwa yankunan da abin ya shafa,” in ji Mbah.

Injiniya Nafisatu Ali daga TCN, ta bayyana cewa ‘yan ta’adda ne suka lalata layin wutar Shiroro-Kaduna, wanda ke bai wa yankin Arewa wuta.

Ta jaddada cewa bai kamata a tura injiniyoyi ba tare da jami’an tsaro ba saboda hare-haren da ake kai wa yankin da wutar ta lalace.

Ta nemi al’ummar yankin da matsalar rashin wutar ta shafa da su ƙara haƙuri, domin ba za a jima ba wuta za ta dawo.

TCN, ya bayyana cewar jami’an tsaro na gadin injiniyoyinsu wanda ke aiki ba dare ba rana don tabbatar da an gyara wutar a kan lokaci.

Mbah, ya bayyana cewa rashin wutar da ake fama da shi a jihohin Arewa ya faru ne sakamakon lalacewar layin wutar Shiroro-Mando.

Rashin tsaro a yankin ya jinkirta aikin da ake yi domin dawo da wutar lantarkin.