Muna aikin inganta harkokin kiwon lafiya a Jihar Nasarawa – Dokta Ikrama
Dokta Hassan Ikrama shi ne Babban Daraktan Asibitin Kwararru na Jihar Nasarawa wato Asibitin Dalhatu Araf da ke Lafiya. A tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana yadda shirye-shiryen sabon Gwamnan Jihar Injiniya Abdullahi Sule ke kawo ci gaba a asibitin: Yaya za ka kwatanta shirye-shiryen Gwamna Abdullahi Sule a bangaren kiwon lafiya? Idan ana batun […]
Dokta Hassan Ikrama shi ne Babban Daraktan Asibitin Kwararru na Jihar Nasarawa wato Asibitin Dalhatu Araf da ke Lafiya. A tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana yadda shirye-shiryen sabon Gwamnan Jihar Injiniya Abdullahi Sule ke kawo ci gaba a asibitin:
Yaya za ka kwatanta shirye-shiryen Gwamna Abdullahi Sule a bangaren kiwon lafiya?
Idan ana batun shirye-shiryen gwamnatin jihar nan a fannin kiwon lafiya zan iya cewa babu shakka Mai girma Gwamna Abdullahi Sule yana da kyakkyawan shiri a bangaren. Kuma hakki ne da ya rataya a wuyanmu a matsayinmu na mukarrabarsa mu tabbatar mun aiwatar da wadannan shirye-shirye. A wasu lokuta gwamnatin jiha takan yi koyi ne da shirin Gwamnatin Tarayya a fannin kiwon lafiya kamar yadda na bayyana a wasu lokuta kuma takan kirkiro da nata shirye-shirye da suka dace da jihar nan da sauransu. Abin da gwamnati ke yi ke nan a yanzu musamman a fannin kiwon lafiya na shirin ta-fi- da-gidanka da sauran manyan hukumomin kiwon lafiyanmu da sauransu a jihar nan. Amma babban shirin gwamnati shi ne a tabbatar an samu ingantaccen kiwon lafiya a farashi mai sauki ga al’ummar jihar nan baki daya. Don bai kamata a ce jama’a ba sa iya samun ingantaccen kiwon lafiya saboda rashin kudi ba. Haka a nan Asibitin Kwararru na Dalhatu Araf muna kokari wajen yin koyi da abin da Mai girma Gwamnan ke yi a fannin don jama’a su samu kiwon lafiya ingantacce a farashi mai sauki. Kuma muna inganta ayyukan kiwon lafiya a nan ta tsarin gwamnatin jihar nan. A da idan an fuskanci matsalar rashin lafiya mai tsanani akan tura Babban Asibitin Kasa ne da ke Abuja da sauransu. Amma yanzu muna kokari mu canja lamarin, tunda muka zo musamman ta inganta kayayyakinmu da ma’aikatanmu da sauransu. Muna kuma rage almubazaranci kuma zan iya cewa muna samun ci gaba matuka a bangaren kawo yanzu.
Wadanne kalubale kuke fuskanta a asibitin tun zuwarka?
Kamar yadda ka sani wani abu mai wuya a rayuwar nan shi ne canji. Mutane sukan ki amincewa da canji a koyaushe. Misali idan suka saba da wani abu sai ka zo ka ce za ka canja wannan abu ka ga dole ne a samu matsala. A da ana gudanar da harkokin asibitin nan ba bisa ka’ida ba amma a yanzu muna kokarin canja lamarin yadda ya dace. Misali halin ma’aikatanmu ga marasa lafiya shi ne babban kalubalen da muke fuskanta. Mutum zai zo ba ya da lafiya sai ka zo kana yi masa ihu ba ka biya masa bukata ba, maimakon haka sai kana ci masa mutunci. Hakan yana kara masa damuwa maimakon magance matsalarsa. Muna so mu canja ra’ayin ma’aikatanmu a wannan bangare. Muna so su fahimci cewa mara lafiya tamkar sarki ne da ke bukatar kulawarsu a nan. Saboda sanadiyarsu ne ake biyanmu albashi da sauransu. Abu na biyu kuma shi ne batun rashin gaskiya da rikon amana da almubazaranci da cin hanci da rashawa da sauransu. A kan haka ne ya sa da zuwana na kirkiro da wani shiri na musamman na yin amfani da wata na’ura ta musamman da ke nadar abubuwan da ma’aikacin asibitin nan ke yi a dukkan bangarorinmu da ake gudanar da ayyuka. Koda yake yawancin ma’aikatanmu suna gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da rikon amana amma akwai wadansu batagari kalilan da ke hana ruwa gudu. Ire-irensu muke kokari mu dakile ayyukansu don samun ci gaba a asibitin kamar yadda ake bukata. Saboda haka a takaice babban kalubalen da muke fuskanta ke nan wato rashin aminci ko rungumar canji daga wadanda suka saba da ayyukan ta’asa a asibitin nan. Amma a hankali muna shawo kan lamarin. Mun samu dimbin nasarori kawo yanzu da suka hada da karin ingantattun kayayyakin aiki da yawa a dukkan bangarori, kamar fannin aikin tiyata da hakan kan rage lokaci da marasa lafiya ke jira likita da sauransu. A yanzu muna da likitocin da ke kula da cututtuka da suka shafi zuciya da a da ba su da na’urorin da ke kula da su, ba sa kuma da isassun likitoci. Muna da isassun kayayyaki kuma a bangaren yara akwai na’urori na musamman da muka sayo musu a fannin don kula da jariran da aka haifa cikin kwanaki kalilan. Na zo na tarar da kayayyakin ba sa aiki amma a yanzu suna yi kuma mun sayo sababbi. Za a iya zagaya da kai idan kana da lokaci don ka gane wa idanunka wadannan abubuwa da nake bayyana maka. Kuma a yanzu muna da kimanin na’urorin gwaje-gwaje na zamani guda shida a shiyyoyi shida a nan, wadanda asibitocin kasar nan da ke da ire-irensu ba su da yawa. Saboda haka zan iya cewa mun kawo canji a kusan dukkan shiyoyinmu yadda ake bukata kuma za mu ci gaba da yin haka har sai hakarmu da burin Gwamna Abudullahi Sule na samar da ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar jihar nan a farashi mai sauki ta cimma ruwa.
Ko kana da wani sako ga al’ummar jihar?
Ka san wani lokaci idan kana so ka kawo canji sai a hankali kamar dai yadda na bayyana a baya. Kamar yaro ne idan kana fasa masa maruru zai yi masa zafi a lokacin amma idan ka gama zai samu sauki. Saboda haka jama’a su yi hakuri su bi mu a hankali don muna kokarin inganta harkokin asibitin ne ta yadda za su more shi. Shi ya sa a wasu lokuta sababbin shirye-shiryenmu suna da wuya ga al’umma da wadansu ma’aikatanmu, amma a karshe kowa zai amfana. Kuma mun sha alwashin inganta harkokin asibitin nan fiye da yadda muka tarar da shi. Ina kuma so in yi amfani da wannan dama in sanar da al’ummar jihar nan cewa a yanzu mun fara horar da ma’aikatanmu na musamman don su zama masu ba da shawarwari kan batuttuwan da suka shafi kiwon lafiya da sauransu. Kuma kafin ka iya yin haka dole sai hukumomi da ke tantance wadannan shiyoyi namu sun tantance ka. Kuma mun gayyace su sun zo sun tantance dukkan shiyoyinmu kafin muka fara gudanar da horarwar.