Muna bayar da harajin miliyoyin Naira ga Jihar Gombe – Kungiyar ’Yan Acaba

Kungiyar ’Yan Acaba da Keke NAPEP ta Kasa (NACTOMORAS), reshen Jihar Gombe ta ce tana samar wa gwamnati kudin shiga na miliyoyin Naira duk shekara. Shugaban Kungiyar NACTOMORAS ta Karamar Hukumar Gombe,  Malam Kabiru Jafaru ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da Aminiya a Gombe. Ya ce duk da wannan kudin shiga da suke […]

Muna bayar da harajin miliyoyin Naira ga Jihar Gombe – Kungiyar ’Yan Acaba

Malam Kabiru Jafaru

Kungiyar ’Yan Acaba da Keke NAPEP ta Kasa (NACTOMORAS), reshen Jihar Gombe ta ce tana samar wa gwamnati kudin shiga na miliyoyin Naira duk shekara.

Shugaban Kungiyar NACTOMORAS ta Karamar Hukumar Gombe,  Malam Kabiru Jafaru ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da Aminiya a Gombe.

Ya ce duk da wannan kudin shiga da suke samar wa gwamnati; suna fuskantar matsalar barayin babura da a kullum suke matsa musu musamman a fadar jihar.

Malam Kabiru Jafaru, ya ce wani lokaci barayin suna kashe musu mambobi; yayin da wani lokacin kuma ake yi musu rauni amma hukuma ba ta yin komai a kai; sannan masu baburan kuma su sa dan acabar da aka kwace babur a hannunsa ya biya su babur din.

Ya ce fiye da shekara ke nan suna bin jami’an tsaro su gurfanar da wadanda ake zargi suna kwace baburan ’yan acaba tare da gano su wane ne suke ba su hodar Ibilis da suke amfani da ita da masu buga musu rasidai na bogi su sayar da baburan da suke kwacewa, amma wannan ya gagara; hakan ta sa suke ganin barayin suna da gata.

Malam Kabiru Jafaru, ya ce kullum suna gaya wa mambobinsu su guji goyon mutum biyu don kauce wa daukar barayi. Kuma suna gaya musu muhimmancin tsayawa a wutar kan hanya don gudun aukuwar hadari

“A Karamar Hukumar Gombe kadai, inda nake shugabanci muna da babura da muka yi wa rajista sama da dubu 19; amma yawan mambobinmu sun fi haka saboda wani babur din mutum biyu zuwa uku ne suke aiki da shi,” inji shi.

Ya ce dalilin da ya sanya ya ce suna tara wa gwamnati harajin da ya kai Naira miliyan 30 a shekara, shi ne duk babur daya suna yi masa rajista ne a kan Naira 1,200, sa’annan idan shekara ta yi za su sabunta rajistar a kan Naira 1,500 kan  babura dubu 19.

Ya yi kira ga gwamnati ta samar musu da babura a farashi mai sauki da za su taimaka musu wajen kara rage zaman kashe wando a tsakanin matasa.

Ya yi kira ga mambobinsu cewa su zama ’yan kasa nagari, domin kiyaye doka tunda su masu biyayya ne ga gwamnati.