Muna buƙatar Gwamna Zulum ya rage cunkoson makabartu — Shehun Borno
Shehun Borno ya yi kira ga jama’a da su riƙa amfani da sauran makabartu da ke cikin unguwanninsu.
Mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar Garbai El Kanemi, ya roƙi Gwamna Babagana Zulum da ya rage cunkoson a manyan makabartun Maiduguri, babban birnin jihar.
Shehun Borno ya yi kiran da a taimaki al’ummar birnin Maiduguri ta hanyar ware fili domin gina makabarta ta biyu domin rage cinkoso a tsohuwar makabartar Gwange da ake amfani da ita tun daga shekarar 1972 zuwa yau.
- Yadda wani ya aurar da ’ya’yansa mata biyu ga malaminsa ‘lokaci guda’
- ’Yan sanda sun kama masu buga jabun kudi 12 a Gombe
Ya bayyana cewa, majalisar masarautar Borno na wannan kira ne biyo bayan korafe-korafen da jama’a ke yi na cunkoso a makabartun babban birnin.
A jawabin da ya yi wa manema labarai a fadarsa, Mai Martaba ElKanemi ya ce Masarautar ta yi wannan kira ne bayan gudanar da bincike kan adadin makabartun da ake da su a cikin birnin Maiduguri da zummar yi wa tufkar hanci.
Ya ce makabartar Gwange da ke kusan tsakiyar birnin na Maiduguri an shafe sama da shekaru 72 ana amfani da ita.
Aminiya ta ruwaito basaraken yana kira ga jama’a da su riƙa amfani da sauran makabartu da ke cikin unguwanninsu maimakon tafiya mai nisa zuwa babbar makabartar ta Gwange.
“A bisa binciken da muka gudanar mun gano cewa babu inda za a binne wani mamaci ya zuwa yanzu a makabartar ta Gwange.
“Saboda haka ne na umurci majalisar nan ta tattara jerin sunayen makabartun da ake da su a birnin Maiduguri da wadanda aka yi watsi da su, domin mu ɗauki matakin da ya dace,” inji Shehu.
Shehun na Borno ya koka da yadda a Karamar Hukumar Maiduguri da Karamar Hukumar Jere kaɗai akwai makabarta sama da dari da ashirin da shida da ko dai ba a amfani da su ko kuma aka yi watsi da su, kuma a madadin haka jama’a na ci gaba da mayar da hankali a kan makabartar Gwange domin binne mamatan ko da daga nesa ne.
Ya kuma bukaci gwamnatin jihar da masu hannu da shuni da su samar da kayan aiki na yau da kullum a makabartun da aka yi watsi da su domin karfafa gwiwar mutane yin amfani da wasu makabartu.
Basaraken ya kuma yi gargadin cewa ci gaba da yin amfani da Makabartar Gwange duk da cunkoson da ta ke da shi zai iya haifar da bullar wata cuta wanda hakan zai shafi al’ummar unguwanni da ke makwabtaka da ita.
Kazalika, ya yaba wa Gwamna Zulum bisa samar da ababen more rayuwa ga al’ummomi daban-daban da kuma tallafa wa ‘yan gudun hijira da marasa galihu a faɗin jihar.