Muna bukatar allurar rigakafi miliyan 6 don yakar Diphtheria a Kano — Abba
Gwamnan ya bukaci karin hadin kai daga gidauniyar game sa sha’anin kiwon lafiya a jihar.
Gwamnatin Jihar Kano ta ce tana bukatar allurar rigakafi miliyan shida domin yaki da cutar Diphtheria mai saurin kisa a jihar.
Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ne, ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin wakilan gidauniyar Bill & Melinda Gate a gidan gwamnatin jihar.
- Kudaden da ministocin Tinubu za su lakume
- Yadda aka yi jana’izar sojojin Nijar da ’yan ta’adda suka kashe
Gwamnan wanda mataimakin gwamnan jihar ya wakilta, ya jaddada aniyar jihar na inganta harkokin kiwon lafiya a fadin jihar.
Ya kuma jaddada aniyarsa na karfafa hadin gwiwa na tsawon shekara 11 tsakanin gwamnatin Kano da gidauniyar Bill & Melinda Gates.
Jami’in yada labaran mataimakin gwamnan jihar, Ibrahim Garba Shuaibu, ya ce gwamnan ya nuna godiyarsa ga gidauniyar bisa tallafin da ta ke bayarwa a fannin kiwon lafiya tare da nuna sha’awar ganin gidauniyar ta tsunduma cikin harkokin noma na zamani.
Mista Jerremy Zungurana, shugaban tawagar gidauniyar ta Najeriya, ya yaba da hadin gwiwar da aka samu tare da yaba wa kokarin jihar a fannin kiwon lafiya.
Ya kuma yi alkawarin bayar da tallafi mai dorewa ga ayyukan jihar kamar yadda gwamnan ya bukata.
A kwanakin baya ne gwamnatin jihar ta kafa cibiyoyin kula da marasa lafiya guda uku a matsayin wani mataki na dakile yaduwar cutar diphtheria a jihar.
Wannan na zuwa ne yayin da jihar ta samu rahoton wadanda suka kamu da cutar sama da mutum 130 a baya-bayan nan.