Muna bukatar sauyi a Jihar Kano

Ra’ayina ya dace da na marigayi Sardauna, Ahmadu Bello, inda yake cewa: “Nakan yi abu ne ta hanyar la’akari da ra’ayina da kuma abin da addinina ya ce.” Na yi zabe a zabubbukan 2011 da 2015, lokacin da kowa ya fi mayar da hankali kan jam’iyya mai mulki da kuma babbar jam’iyyar adawa. Baya ga […]

Muna bukatar sauyi a Jihar Kano
Muna bukatar sauyi a Jihar Kano

Ra’ayina ya dace da na marigayi Sardauna, Ahmadu Bello, inda yake cewa: “Nakan yi abu ne ta hanyar la’akari da ra’ayina da kuma abin da addinina ya ce.” Na yi zabe a zabubbukan 2011 da 2015, lokacin da kowa ya fi mayar da hankali kan jam’iyya mai mulki da kuma babbar jam’iyyar adawa. Baya ga wadannan biyun, sauran jam’iyyun kawai “suna” suka tara a siyasar Najeriya.

’Yan Najeriya, a matsayinsu na ’yan kasar da ke amfani da tsarin jam’iyyu da dama, suna da damar su zabi dan takara saboda kokarinsa, ba saboda jam’iyyar da ya tsaya takara a cikinta ba. Wadansu mutanen za su iya cewa amfani da tsarin siyasa mai jam’iyyu biyu, bai dace da tsarin dimokuradiyya ba, saboda zai hana mutane masu nagarta fitowa takara saboda rashin jam’iyyar da za su fito a karkashinta.

A matsayina na mai lura da al’amura, kullum ina jajircewa ne don ci gaban wannan kasa. Daga cikin jajircewar nan kuwa akwai fitowata takara a wannan zabe mai zuwan domin mika gudunmawata.

Na fahimci cewa, mutum zai iya sa kansa cikin ayyuka na ci gaba irin su ayyukan kungiyoyin jinkai (NGOs) domin samun sauyi a wannan kasa. Mutum zai iya kokarinsa, amma zai fi yin kokari ne idan yana da ragamar mulki a hannunsa. Wannan har yanzu shi ne ra’ayin Malam Nasiru El-Rufa’i, Gwamnan Jihar Kaduna.

Tunda Najeriya ta dawo  dimokuradiyya, ’yan Najeriya suna mayar da hankalinsu ne kan jam’iyyu biyu manya, har ma suna cewa jefa kuri’a wa wata jam’iyya da ba mai mulki ko kuma babbar jam’iyyar adawa ba, kamar asarar kuri’a ce. Sai dai ba haka abin yake ba a yankin Yarbawa na Kudu maso Yamma inda jam’iyyu sama da daya ko biyu suke da armashi. Ai mun ji labarin AD da ACN da kuma Labour Party; wacce ta samu Gwamna a Jihar Ondo. A Arewacin Najeriya kuma, CPC ta dan samu karbuwa saboda ta samu miliyoyin kuri’u, har ma ta samu gurbin ’yan majalisun jiha da na wakilai da na dattawa a zaben 2011. Hasali ma har kujerar Gwamna ta samu a Jihar Nasarawa.

Daga shekarar 2015, ba ka jin duriyar wata jam’iyya in ban da APC da PDP. Gaskiya lokaci ya yi da za mu nuna wa duniya jam’iyya ba ita ce nagarta ba.

A Kano, tasirin jam’iyyu biyu (APC da PDP) ya yi yawa. Lokaci ya yi da mutanen “Cibiyar Kasuwancin” za su fadakar wajen samar wa kansu shugabanci nagari domin al’amura sun bayyana cewa akwai yaudara da son kai a cikin manyan jam’iyyun.

Duk da cewa an samu ci gaban kayan more rayuwa a karkashin gwamnatin Ganduje, bidiyon da ya nuno shi yana karbar na-goro ya isa hujja a ki zabarsa. Idan muka dubi abin sosai, bai ma kamata ya fito neman kujera ba balle a tsayar da shi dan takara. Cin hanci dai kowane iri ne, cin hanci ne kuma abin Allah wadai ne.

Abba Kabir Yusuf na PDP kawai zai zama dan amshin Shatan Kwankwaso ne idan ya zama Gwamna.

Son kai da jiji-da-kai irin na Kwankwaso su suka kawo Abba Kabir duk da cewa a bayyane yake, tare da Kwankwaso, akwai ’yan takara da suka fi Abba nagarta. Amma saboda son-kai da burin komawa wa’adin mulki na uku (a kaikaice) sai kawai ya kakaba wa mutane surukinsa, wato Abba.

Ina son tsayayyen Gwamna ne wanda ba ya karba ko bayar da cin hanci, kuma wanda idan ya zama Gwamna; burinsa shi ne yadda za a yi a ciyar da Jihar Kano gaba.

Muhammad Salihu Sagir Takai mutum ne mai kwazo wanda ban taba gamuwa da shi ba – kawai labarinsa nake ji. Burinsa na kawo sauyi a Jihar Kano, mayar da kananan hukumomi su koma cin gashin kansu da kuma ba wa kowane jami’i ikonsa a gwamnatance, wadannan sun kai su zama dalili na cewa Takai zai sauya Jihar Kano.

Ita “karamar hukuma” ta fi kusanci da jama’a. Saboda haka, rashin ba ta damar cin gashin kanta ne ya sa ba ma ci gaba a fagen kiwon lafiya da ilimi da sauransu.

Munanan yanayin da cibiyoyin lafiya a matakin farko da makarantu suke ciki sun auku ne sakamakon rashin bai wa kananan hukumomi ’yancin cin gashin kansu. Kuma na bibiyi muradun Takai game da bai wa kananan hukumomi damar cin gashin kansu. Tun yana kwamishina yake da wannan kudiri. Kuma a matsayinsa na tsohon shugaban karamar hukuma, zai yi matukar kokari – yadda ba a tsammani.

Yayin da na ga nasarorinsa lokacin da yake Shugaban Karamar Hukumar Takai kuma kwamishina, ya aiwatar da abin a-zo-a-gani.

Sannan Takai, a matsayinsa na dan takarar Jam’iyyar PRP, ba wani ne ya kakaba shi a kan jama’a ba. Ke nan, wannan alama ce da ke nuna Allah zai albarkaci Jihar Kano da Gwamnan da ba dan amshin-Shatan wani ba.

Don haka ina ganin Salihu Sagir Takai a matsayin mafita a zaben Gwamnan Jihar Kano, ba Ganduje na APC ko Abba Kabir na PDP ba.

Kada mu bari jam’iyya ta yi mana tasiri. Abin dubawa dai ita ce nagartar dan takara.

Za mu samu ci gaba ne kawai idan muka fahimci cewa Jihar Kano ba wata jam’iyya ko wani uban gida take bukata ba.

 

Adnan Tudunwada dan jarida ne, kuma za a iya samunsa ta Tuwita: @adnanmoukhtar.