Muna ci gaba da kokarin kubutar da sauran ’yan matan Chibok –Buratai
Hafsan Hafsoshin Sojin Najeriya Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai ya ce har yanzu sojoji suna kokarin ganin an kubutar da ragowar ’yan matan Chibok da suke hanun ’yan Boko Haram. Janar Buratai ya yi wannan jawabi ne a wajen wani taron karawa juna sani a kan sha’anin tsaro da aka gudanar a Jami’ar Igbinedion da […]
Hafsan Hafsoshin Sojin Najeriya Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai ya ce har yanzu sojoji suna kokarin ganin an kubutar da ragowar ’yan matan Chibok da suke hanun ’yan Boko Haram.
Janar Buratai ya yi wannan jawabi ne a wajen wani taron karawa juna sani a kan sha’anin tsaro da aka gudanar a Jami’ar Igbinedion da ke Okada a Jihar Edo.
Ya ce Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari tare da hadakar dakarun yankin Tafkin Chadi (MNJTF) sun bayar da gudunmawar Dala miliyan 100 domin fadada ayyukan rundunar.
Janar Buratai ya kara da cewa rashin isasshen tallafi daga kasashen waje na kawo cikas a yakin da ake yi da ta’addanci.
“Daya daga cikin abubuwan da muka sanya a gaba shi ne canja wa sojojinmu fasali maimakon su zama masu kare kai daga farmakin makiya su zama masu kai farmaki. Sannan mun samar da wani sashe da zai rika tallafa wa duk rundunar da take a bakin fama,’’ inji shi.
Ya ce a yanzu harkokin yau da kullum sun dawo a wasu yankuna, inda za a ga jama’a suna ci gaba da harkokinsu babu tsangwama. Ya ce wannan ci gaban da aka samu ya ta’allaka ne da irin gudunmawar da sojoji da sauran jami’an tsaro suka bayar wajen wayar da kan al’umma.
Ya ce ga dukkan alamu an samu ci gaba a siyasar Najeriya idan aka yi la’akari da irin gudunmawar da sojoji suke bayarwa ta hanyar bin tsarin mulkin Najeriya.