Muna ci gaba da tattara bayanai kan kashe-kashe a Kano — ’Yan sanda

Muna godiya ga masu bamu bayanai a cewar rundunar ‘yan sandan Kano.

Muna ci gaba da tattara bayanai kan kashe-kashe a Kano — ’Yan sanda

DSP Haruna Abdullahi Kiyawa

Rundunar ’yan sandan Kano ta sanar da cewa tana ci gaba da tattara bayanai dangane da rahoton kisan mutane da ake samu a wasu unguwanni a jihar.

A baya nan dai wasu rahotanni na cewa ana fargabar an kashe mutane yayin wata arangama a ranar Asabar tsakanin jami’an tsaro da wasu mazauna unguwannin Kurna da Rijiyar Lemo da ke Karamar Hukumar Fagge a jihar.

Cikin wani sako da ya wallafa shafinsa na Facebook, mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce suna ci gaba da bin diddigi da tattara bayanai a kan lamarin.

“Game da abin da ya faru a Unguwar Kurna da Rijiyar Lemo a ranar [Asabar] 03/08/2024, muna tattara bayanai domin sanin gaskiya da kuma yin bincike in sha Allahu.

“Muna godiya ga masu bamu bayanai,” inji sakon da Kiyawa ya wallafa.

Aminiya ta ruwaito cewa akalla mutum tara zuwa 10 ne rahotanni ke cewa sun mutu a unguwannin Kurna da Rijiyar Lemo da Bachirawa da kuma Kofar Nassarawa duk a kwaryar birnin Dabo.

Haka kuma, wasu dama ana fargabar cewa sun samu raunuka a yayin da wasu masu zanga-zangar tsadar rayuwa suke bijire wa umarnin gwamnati da sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 har suka mamaye tituna.

Rahotanni na zargin cewa jami’an tsaro sun yi harbe-harbe a kokarinsu na tarwatsa masu zanga-zangar, lamarin da ya yi sanadin rasa rayukan jama’a

Har kawo yanzu dai ana ci gaba da zaman dar-dar a wadannan unguwanni da jama’arsu suka bijire wa dokar hana fita a kokarinsu na ci gaba zanga-zangar tsadar rayuwa da aka soma tun ranar Alhamis a fadin kasar.

Sai dai gwamnatin jihar ta sanar da sakar wa al’ummar jihar mara, inda ta sassauta dokar hana fitar a yau Lahadi da karfe 8:00 na safe zuwa 2:00 na rana.