Muna da ja kan dokar takaita wa’azi – Sheikh Babantune
Sheikh Abubakar Usman Babantune Shi ne Shugaban Majalisar Malamai da Limamai ta Jihar Kaduna, a tataunawarsa da manema labarai kan shirin da gwamnatin jihar ke yi na fitar da dokar takaita wa’azi ya ce ba za su yarda da duk dokar da za ta cutar da Musulunci ba: Aminiya: A kwanaki gwamnatin Jihar Kaduna ta […]
Sheikh Abubakar Usman Babantune Shi ne Shugaban Majalisar Malamai da Limamai ta Jihar Kaduna, a tataunawarsa da manema labarai kan shirin da gwamnatin jihar ke yi na fitar da dokar takaita wa’azi ya ce ba za su yarda da duk dokar da za ta cutar da Musulunci ba:
Aminiya: A kwanaki gwamnatin Jihar Kaduna ta mika wani kuduri ga Majalisar Dokokin Jihar na neman sanya wasu ka’idoji kan harkokin addinai a jihar. Yaya kuke ganin wannan yunkuri?
Kamar yadda na fada wa rediyon BBC da sauran kafafen watsa labarai, mun ji wannan doka kamar yadda kowa ya ji. Amma a lokacin da dokar ta zo hannunmu sai muka yi kokarin saduwa da wanda dokar ta shafa, wato bangaren gwamnati, muka sadu da su muka fada masu abin da muke gani, kuma muka tabbatar masu cewa ba ya yiwuwa a kafa doka a kan abin da ya shafi addini, ba tare da tunanin malamai suna da ta cewa a kai ba. Amma sai gwamnati ta tabbatar mana da cewa wannan doka ta fita a hannunsu, ta koma hannun majalisa. Saboda haka sai wannan majalisa da nake shugabanta ta rubuta takarda zuwa ga Shugaban Majalisar Jihar Kaduna, cewa muna son mu san me wannan doka ke ciki. Kuma alhamdulillahi, majalisa ta nemi mu je mu zanta da ita, muka zanta da su, suka tabbatar da cewa ba za a kafa wannan doka ba sai da shawarar malaman addinai. Suka tabbatar da cewa majalisa ba za ta yi wani abu a kan dokar ba, sai sun ji daga bakin malamai, sun ga mene ne maslaha ga al’umma. Saboda haka wannan ya sa yanzu ba za mu iya cewa kowai game da dokar ba, domin muna da ra’ayoyi a kan abin da za mu fadi game da dokar. Da farko dai akwai kura-kurai masu yawa a cikinta da suke bukatar gyara. Ba za mu iya gaya wa mutane a jarida irin gyaran ba a yanzu. Amma dai akwai gyare-gyare a ciki, da suke masu tsanani kwarai. Akwa sassan da suka kamata a soke su, akwai abubuwan da wannan majalisa za ta yi kokarin ganin cewa lallai ta ankarar da gwamnati a kansu.
Lokacin da dokar ta zo hannunmu, Majalisar Malamai da Limamai ta Jihar Kaduna ta sa an fassara ta zuwa Hausa, domin da Turanci aka rubuta ta, kuma duk malamai da limaman da ke jihar da muka san fitattu ne, kuma za su fahimci abin da ake yi, mun ba su. Kuma muka ce su karanta, bayan sun karanta, sun zo mun yi taro da su. Muka kafa kwamitin da zai bi dokar nan ciki da waje, sannan ya bayar da mafita a kai.
Amma a gaskiyar magana, ’yan majalisa sun yi abin da ya kamata su yi, domin sun tabbatar wa malamai cewa ba za su yi wani abu ba, sai bayan malaman addinin Kirista da na Musulunci sun duba dokar ciki da waje, sun bayar da shawara. Kuma sun nuna cewa lallai za a saurari maganganun masu addini, wannan ita ce matsaya. Yanzu misali, kamar yadda na ce akwai kura-kurai a ciki. Watakila wani ya ce wadanne ne kura-kuran ne? To, suna da yawan gaske! Misali, akwai wani sashi a cikin dokar da ke nuna cewa za a yi wani kakkarfan kwamiti, wanda shi ne ke da bakin magana a kan kingiyoyin Jama’atu Nasril Islam da ta Kiristoci (CAN), inda su ne za su rika bayar da lasisi ga wadannan kungiyoyi biyu.
Aka ce Mai girma Gwamna ne zai kafa wannan kwamiti, shi ne kuma zai nada shugabansa, kuma wanda zai shugabanci kwamitin, ba zai gaza Mai ba Gwamna Shawara kan Harkokin Tsaro ba.
Sannan mambobin kwamitin, akwai wakili daga Ma’aikatar Shari’a ta Jihar da wakili daga ’yan sanda da ba zai gaza matsayin Sufurtanda ba, akwai daga Hukumar Tsaro ta DSS, akwai wakili daga Hukumar Cibil Defence, akwai wakili daga JNI, akwai kuma daga CAN.
To, in ka tara wadannan wakilai da aka yi magana, wadanda ke da dangantaka da addini, wanda ke wakiltar Musulunci mutum daya ne tak, haka wanda ke wakiltar Kirista mutum daya ne. To kuma sai aka ce wadannan ne ke da bakin magana a kan wa’azi a jihar nan. Wannan na kawo misali ne, abubuwan suna da yawan gaske. Sannan a doka, a ce bayan karfe takwas na yamma, ba a yarda a ji amsa-kuwwa na magana a duk fadin jihar ba. To wannan kuskure ne, kuma akwai irinsu da yawa, ba wai muna so mu fadi abin da za mu ce, ko abin da za mu yi ba ne. Amma bin da ya sa na fadi wannan, domin matashiya ce cewa akwai kura-kurai a ciki. Mun san manufar gwamnatin ita ce gyara, ta ga cewa an sa komai bisa ka’ida, wannan yana da kyau. Amma matukar ba a bi hanyar da ta dace wajen gyara ba, to tana iya zama barna.
Aminiya: Malam ya ce su ma sun ji ne kamar yadda kowa ya ji. Wannan ya nuna ba a tuntube ku ba ke nan kafin a kafa dokar?
Eh to, ina ganin kamar yadda na yi wannan magana, a bar ta a haka. Domin akwai wasu abubuwa da bai kamata mu zo mu fada wa mutane ba. Akwai wasu kura-kurai da ake yi. A ka’ida, duk gwamnatocin tarayya da na jihohi a nan Arewa, in za su yi hulda da wata kungiya ta addinin Musulunci, ita ce Jama’atu Nasril Islam, in na Kirista ne, CAN. To su wadannan kungiyoyi biyu, CAN da JNI, ya kamata ne su yi abin da ya dace. Idan aka ce ana neman abin da ya shafi har za a yi doka a kan wa’azi, to ya kamata JNI ta nemi wadanda ya dace, ta nemi malaman da suka dace ta yi hulda da su. Abin da ya kamata a yi ke nan. In da an yi haka, to ba za a samu wani ka-ce-na-ce ba. Kuma wadannan kura-kurai ne muke so a gyara. A shirye muke, kuma za mu bayar da gudumawa a gyara.
Aminiya: Tunda abin ya bar hannun gwamnati, wace shawara Malam ke da ita ga Majalisar Dokokin?
Kamar yadda na fada, za mu duba dokar nan ciki da waje, kuma za mu ba su shawara, kuma ba za mu taba yarda a zartar da wata doka, da ta ke akwai kuskure ko za ta cutar da addinin Musulunci ba. Amma majalisarmu za ta yi kokari ta ga duk wani abin da zai kawo maslaha ga al’umma, a ga an sa mutane a kan saiti, za mu tabbatar da shi. Amma duk abin da zai zama a cikinsa akwai kura-kurai, sai an gyara. Wato abin da ke faruwa, ba zai taba yiwuwa ba a ce kowace gwamnati, in ta ga dama a kan abin da ya shafi addini, alhali ba ta taimakon addinin nan, ba ta da wata dangantaka da addinin, kawai ranar da ta ga dama ta ce ta sa doka haka kawai, shi ke nan kuma sai a yi mata biyayya? Malamai su yi mata biyayya? Abin da ya sa na ce ba ta yi wa addini komai, domin gwamnatin nan ba ta Musulunci ba ce, ba ta da wani kaso da ta ware wa wani addini wanda ake taimaka masa. Misali, a ce gwmnati za ta dauki nauyin gina Islamiyya, ita za ta dauki nauyin malamai masu karantarwa da horar da su da sauransu. Idan da tana haka, to tana da bakin magana a kansu, amma haka kawai da rana tsaka za ta kafa doka, to dole ta tuntubi wadanda al’amarin ke hannunsu. Saboda haka a shirye muke mu bayar da kowace irin gudumawa insha Allahu.